Vision FM: SERAP ta bai wa Gwamnatin Buhari sa’o’i 24 kan ta janye matakinta ko ta maka ta a kotu

“Matakin da gwamnatin Buhari da NBC suka ɗauka, wata alama ce da ke nuni da take-taken da ake yi na neman yi wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu kisan mummuge da hana ɗaiɗaikun mutane ‘yancin faɗar albarkacin bakinsu” – SERAP

Daga BASHIR ISAH

Ƙugiyar SERAP ta ce babu abin da zai hana Hukumar Kula da Gidajen Rediyo ta Ƙasa (NBC) fuskantar matakin shari’a cikin sa’o’i ashirin da huɗu sai dai idan ta janye tarar Naira miliyan 5 ɗin da ta yanka wa gidan rediyon Vision FM da ke Abuja.

Idan dai ba a manta ba, Manhaja ta rawaito yadda NBC ta ɗora wa Vision FM tarar milyan N5 tare dakatar da wani shirin tashar mai taken ‘Idon Mikiya’ kan tattauna badaƙalar tsawaita wa’adin aiki na shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIN), Rufai Abubakar.

NBC ta aika wa Vision FM da takarda a hukumance inda ta sanar da ita cewa ta taka mata ɗaya daga cikin dokokinta a cikin shirinta na ‘Idon Mikiya’.

Shirin da NBC ta ce an gudar da shi ne a ranar 5 ga Janairun 2022, a rediyo da kuma talabijin, wato tashar Farin Wata TV.

Da take martani game da wannan mataki da NBC ta ɗauka kan tashar Vision FM a wannan Larabar, SERAP ta bayyana abin da NBC ta yi a matsayin haramtacce wanda kuma ya saɓa wa kundin tsarin mulki. Tare da yin barazanar maka NBC da Gwamnatin Tarayya a kotu muddin suka gagara janye tarar da kuma ɗage dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’ da suka yi a tsakanin awanni 24.

SERAP ta ce, “Matakin da gwamnatin Buhari da NBC suka ɗauka, wata alama ce da ke nuni da take-taken da ake yi na neman yi wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu kisan mummuge da hana ɗaiɗaikun mutane ‘yancin faɗar albarkacin bakinsu.

“Wajibi ne ga gwamanti ta ɗage dakatarwar sannan ta yi riƙo da Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa gyara) da kuma tanade-tanade na ƙasa da ƙasa, sannan ta martaba tare da kare ‘yancin faɗar albarkacin baki, ‘yancin tattara bayanai da kuma ‘yancin yaɗa labarai.”