Waɗanda ke neman ruguza Shi’a ba su yi nasara ba, cewar El-Zakzaky

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, (IMN), Shaikh Ibraheem El-Zakzaky, a makon da ya gabata, ya bayyana cewa, waɗanda ke neman rusa ƙungiyar bayan kisan kiyashin Zariya a shekarar 2015 ba su samu nasara ba.

El-Zakzaky ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa ta farko da wakilan ɓangarori daban-daban na dandalin addini a Abuja.

Ya yi bayanin cewa zaluncin da aka yi wa Harkar Musulunci a Nijeriya, wanda ya cika da shekaru shida na zaman gidan yari, ya mara famtsama sanin ƙungiyar a dukka faɗin a duniya.

El-Zakzaky ya ce, “yayin da aka ƙaddamar da farmakin gaba ɗaya da nufin murƙushe Harkar, ba a yi nasara da wani abu ba face ɗaukaka Harkar zuwa matakin da ba a yi tsammani ba.”

“Za mu iya cewa kisan gillar da aka yi a Zariya a shekarar 2015 wani lokaci ne na gwaji wanda ya shafi jama’a.”

Ya yaba wa dukkan ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na cikin gida da na waje da ƙungiyoyin jin ƙai da ke ci gaba da matsa lamba don a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba daga tsare shi tare da biyan buƙatun mabiyansa, waɗanda suka sami raunuka da asara daban-daban a ƙoƙarin neman ‘yancinsa.

Jagoran na IMN ya jajantawa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu yayin harin sojoji na 2015 a kan ƙungiyar da kuma neman adalci.

Yayi addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi ya kuma sa aljanna ce makomarsu ta ƙarshe.