Waɗanda suka bijiro da batun “halartar Taiwan a taron WHA” sun ji kunya!

Daga IBRAHIM YAYA

Ƙasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin, ita ce kaɗai halastacciyar gwamnati dake wakiltar ƙasar Sin. Haka kuma wanzuwar ƙasar Sin daya tilo a duniya, ita ce babbar manufar da ƙasashen duniya suka amince da ita, kana shi ne tushen siyasa na raya hulda tsakanin Sin da duk ƙasashen da suka ƙulla ko ma suke son ƙulla alaƙa da ƙasar Sin.

Duk da cewa ƙasar Amurka na daga cikin ƙasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da ƙasashen biyu suka aminta da su a kan alaƙar dake tsakaninsu, amma a wasu lokuta ta kan yi biris tare da neman lalata tushen siyasa na hulɗar dake tsakaninta da ƙasar Sin, inda take ci gaba da hulɗa da yankin Taiwan na ƙasar Sin, har da neman sanya ta cikin tsarin hukumomin MƊD, kamar babban taron majalisar kiwon lafiya ta duniya.

Sanin kowa ne cewa, Taiwan ba ƙasa ba ce, wani ɓangare ne na ƙasar Sin. Duk abun da wani kokari na jirkita gaskiya, ko kaɗan ba zai taba yin nasara ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna ƙarƙashin ikon Jamhuriyar Jama’ar ƙasar Sin ne.

A ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da ƙara martaba wannan manufa, babban taron majalisar kiwon lafiya na duniya karo na 75, ya yanke shawarar yin watsi da shawarar da ƙasashe daban-daban suka gabatar, na gayyatar Taiwan zuwa taron majalisar a matsayin ’yar kallo, matakin da masu sharhi ke nunawa ƙarara cewa, manufar ƙasar Sin daya tilo a duniya, ita ce tsarin da al’ummomin ƙasa da ƙasa suka aminta da shi, kuma ba za a iya ƙalubalantarsa ba. Kuma waɗanda suka bijiro da batun “halartar Taiwan a taron” sun ji kunya!

Mahukuntan ƙasar Sin dai na ƙara fahimtar da ƙasashen duniya game da manufar ƙasar Sin daya tak a duniya, duk da cewa, wasu ƙasashe suna sani da haka, amma su kan rufe ido su saba wannan manufa don neman biyan wata buƙata ta kashin kai da neman tayar da fita.

Inda a sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, ta bayyana ƙarara cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da martaba ƙa’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin wannan da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje.

Wannan ya ƙara fayyace tsayin daka na ƙasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar ƙasa da cikakken yankunanta, har ma da tsaro da moriyar ci gabanta baki ɗaya. Ta kuma sha alwashin daƙile duk wani kutsen maƙiya daga waje da nufin kawo mata ɓaraka a cikin gida.

Fassarawa: Ibrahim Yaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *