Waɗanda suka yi garkuwa da ni sun buƙaci Nollywood ta mara wa Nnamdi Kanu baya, inji Jaruma Okereke

Daga AISHA ASAS

A kwanakin baya ne masana’antar finafinai ta Nollywood ta haɗu da tsautsayi, inda masu garkuwa da mutane don amsar kuɗin fansa suka cabke biyu daga cikin jaruman ta, wato Cynthia Okereke da kuma Clemson Cornel, a Jihar Enugu, suna neman a biya su Dalar Amurka 100,000 kafin su sako su.

Idan mai karatu na bibiye da lamarin ya san cewa, a makon da ya gabata ne AGN (Actors Guild of Nigeria) ta tabbatar da shaƙar iskar ancin da suka yi a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, 2022, a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta tabbatar dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.

Biyo bayan haka ne, Jaruma Okereke ta bayyana yadda lamarin ya kasance tun daga kamen zuwa dawowar ta cikin iyalinta. Jarumar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ta yi da Sunday Scoop.

Jarumar ta fara da bayyana kamen da aka yi mata a matsayin kuskure kamar yadda suka sanar da ita, ” sun sanar da ni ba ni ce suka yi niyyar kamawa ba, kuma kamen na wa kuskure ne, sai dai tunda sun kasa samun wanda suke so dole su tafi da ni.”

Game da raɗe-raɗen da ake yi na sai da aka biya maƙudan kuɗaɗe kafin aka sako ta, jarumar ta ƙaryata wani sashe na labarin, sai dai da aka tambaye ta ko nawa ne aka biya kafin su sako ta, jarumar ta ce, “wannan ne ba zan sanar da kai ba, domin ba na buƙatar ya zama abin faɗa, sai dai zan iya tabbatar ma an biya kuɗin fansa kafin a sako ni, kuma mijina ne ya kai kuɗin a Ngwa da ke cikin Jihar Abia.

Da ta ke bayyana irin halin da ta shiga a hannun masu garkuwa da ita, Okereke ta ce, “kwanaki biyun farko da na yi a hannunsu ba su ba ni komai na ci ba. Sai a rana ta uku ne suka ba ni madara da maltina, sai dai daɗewa da cikina ya yi ba abinci ya sa na ƙi sha, saboda na san dole zan yi amai idan ya shiga cikina.”

Da aka tambaye jarumar ko waɗanda suka kamata sun gane ta a matsayin ‘yar fim, ta ce, “lokacin da suka kama mu a Centenary Junction cikin Jihar Enugu, sun ce, “Cynthia Okereke, kina tunanin ba mu gane ki ba ko?” Na ce masu me suke buƙata wurina. A lokacin da suka harba bindiga a sama, na roƙe su, su ɗauki motata, su tafi da ita, suka ce ba sa buƙatar mota.”

Da ta ke amsa tambayar yadda aka kai su inda suka zauna tsayin kwanaki da suka yi, jaruma Cynthia cewa ta yi, “sun ɗaure idonmu da ƙyale, ba mu ga komai ba har sai da suka kai mu wani wuri da ban sani ba. Sai ma da safe ne da ɗaya daga cikin su ya tambaye ni ko na san inda mu ke, na ce a’a, ya ce, mu na cikin Jihar Ebonyi.”

Dangane da wasu batutuwa da masu garkuwa suka yi mata, Cynthia Okereke ta ce, ” sun ce masana’antar Nollywood ba ta goyon bayan Nnamdi Kanu wato shugaban IPOB. Suka ce ya kamata ne mu fito kwai da kwarkwatarmu, mu mara masa baya. A cewar su, faɗan da Nnamdi Kanu yake yi na amfanin dukkanmu ne (ƙabilar Ibo).

A ɓangaren takwaranta a wannan tsautsayi kuwa, wato Clemson Cornel, makusantansa sun tabbatar da yana kwance a asibiti yana karɓar magani, bayanin ya biyo bayan kiran da Sunday Scoop ya yi wa layin jarumin, wani makusancinsa ya ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *