Waɗanda suka zavi Tinubu har sun fara da-na-sani, inji PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP, reshen jihar Ondo, ta ce ‘yan Nijeriya da suka zaɓi Jam’iyyar APC a zaven 2023, tuni suka fara nadamar abin da su ka zaɓa.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ondo, Fatai Adams, a wata sanarwa da ya fitar ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Kennedy Peretei, a Akure, babban birnin jihar.

Adams ya ce zabven Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jawo wa ‘yan Nijeriya wahalhalu, musamman janye tallafin man fetur, wanda ya jefa al’umma cikin halin wahala.

Adams yana maida martani ne kan kalaman takwaransa na Jam’iyyar APC a jihar, Ade Adetimehin, inda ya ce PDP ta mutu.

Da ya ke maida martani, shugaban jam’iyyar PDP ɗin na Ondo ya ce a’a, Jam’iyyar APC da muguwar gwamnatinta ne ya jawo wa ‘yan Nijeriya wahala da raɗaɗin rayuwa cikin shekaru takwas da suka gabata.

Kila Adetimehin shi ne mutum ɗaya tilo da ya manta da cewa al’ummar jihar Ondo suna riƙe da jam’iyyarsa ta APC da gwamnatinta na rashin mutuntawa da alhakin wahala da raɗaɗin da suka shiga cikin shekaru takwas,” inji Adams.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *