Waɗanne mata ne maza ba sa so?

Daga AMINA YUSUF ALI

A wannan mako za mu kawo muku mata da suka zama baragurbin mata waɗanda duk macen da ta kasance cikinsu, abar gudu ce a wajen mutane. Idan ba ta ɗauki matakin gyara ba.

Mace mavarnaciya/al-mubazzara: Ita ce macen da ba ta da tattali da kaffa-kaffa da kayan gida idan mai gida ya kawo. Irin waɗannan mata ba ƙaramin shaqa wa maza baƙinciki suke a zukatansu ba. Musamman maza marasa ƙarfi masu ƙoƙarin ganin sun sauke haƙƙin iyalansu. Ta hanyar ƙuƙutawa su sayo dukkan abinda ake buƙata na gida. Musamman a wannan lokaci na tsadar rayuwa. Namiji ya siyo kayan abinci ya tarar an dafa an ci an zuzzubar ko’ina ba zai ji daɗi ba.

Mace munafuka: Mace munafuka ita ce mace magulmaciya da kullum ba ta da aiki sai shige da fice a gidaje da tsakanin mutane tana yaɗa labarai masu ta da hankali da ta da fitina. Kullum mijinta da yaranta ba kwanciyar hankali. Domin tana farawa daga ƙuruciyarta har zuwa tsufan ta. Ga jawo zub da ƙimar kanta da ta mijinta har ma da yaranta. Musamman idan yaran sun girma.

Mace ƙazama: kamar yadda muka sani, gyara shi ne jigon kowacce mace. Mace ƙazama ita ce wacce ba ta damu da gyara jikinta ko yaranta ko muhallinta ba. Ko’ina ta bar shi kace-kace. Kuma tsafta na ɗaya daga cikin abubuwan da maza suke so. Shi ya sa suka ƙi jinin mace ƙazama. A addinance ma tsafta alkhairi ce. Kuma tana daga cikin abubuwan da suke jawo a so ko a tsani mutum.

Mace mai mita: Mace mai mita ita ce macen da ba ta bari abu ya shige. Ta dinga maimaitawa kenan. Mita ko a kan abinda ba laifi ba ne tana da cin rai. Shi ya sa maza ba sa son wannan matar.

Mai tsananin kishi har da danginsa: Mace mai tsananin kishi mace ce wacce zuciyarta take cike da hassada a cikinta. Ita ce macen da ba ta qaunar ta ga wani ya ravi mijinta ko kuma uwa uba a mori wani abu daga arzikin mijin nata.

Wannan irin mace za ta iya rasa imaninta ko dukiyarta ko ta yi ma kisan kai saboda ɗa namiji. Irin wannan mace sam ba za ta lamunci a karo mata kishiya a gidan ba. Su kansu dangin mijinsa tun daga uwarsa yayye, ƙanne, ba ta ƙaunar ta ga wata harkar arziki ta shiga tsakaninsu da mijinta. Irin waɗannan mata su ne masu azabtar da ‘ya’yan kishiyoyinsu idan sun mutu ko sun bar gidan. Kuma za su iya kai wa ga hallaka yaran ma ko ma mijin kansa gabaɗaya saboda kishi. Domin tsananin kishi da hassada yana kai wa ga rashin imani.

Mara biyayya/ fitsararriya: Kar ki zama mace mara kunya fitsararriya wacce ba ta ganin kowa da gashi. Ba wanda ya wuce ta ci masa mutunci daga iyayenta, ‘yanuwa, saurayi, miji, har ma da dangin miji da sauransu. Irin wannan mace sam ba matar aure ba ce. Kuma abin gudu ce ga dukkan maza masu mutunci.

Mara kamun kai: Mace mara kamun kai ita ce ballagazar mata. Wacce ba ta san ciwon kanta ba. Kullum cikin shigar banza ko shiga mai muni. Ga kule-kulen maza barkatai. Jaki da doki duk samarinta ne. Yawancin waɗannan matan suna fama da rashin mafaɗi. Ga ta da ɗaga sautin murya idan tana magana Wani lokacin ma har ciye-ciye za ta dinga yi a kan hanya. Ga ta ba ta jin kunyar faɗar batsa ko da maza sun kai dubu a waje. ‘yaruwa raba kanki da wannan halayya ta Allah wadai.

Mai girman kai: Ya kamata a kula fa. Girman kai da mutunta kai akwai banbanci. Kuma mutunta kai halayya ce mai kyau. Amma girman kai da izza da jin kin fi kowa ɗabi’a ce ta marasa tarbiyya. Ba a ce ki saki jiki da kowa ki zama ballagaza ba. Amma kada ki dinga wulaƙanci da share mutane.

Mai yawan roqo/ Mai son abin Duniya: Mace mai roqo ita ce wacce ba ta jin kunyar tambayar abu a wajen namiji. Maza sun tsani wannan ɗabi’ar duk da dai suna ba da abinda aka nema ɗin. Ki sani roƙo yana zubar da mutunci. Sannan kuma roƙo da son abin Duniya shi ne silar da mace take faɗawa cikin tarkon samari marasa kirki.

Mara ilimi: Mace marar ilimi kamar ta rako mata Duniyar nan haka take. Ba ta da wata daraja a gurin mutane. Haka ta fuskar ibada ma sai da ilimi ake gudanar da ibada. Sai da ilimi kuma ake tafiyar da al’amura da dama a Duniya. Jahilci duhu ne. ‘Yaruwa ki nemi ilimi, shi ne gishirin rayuwa.

Mara rike sirri: Mace mara sirri da ita da fankon ashana duk saya. Domin bankaɗaɗɗiya ce ita ko sirrin mijinta a fai-fai yake. Ko’ina tana talla da sirrin gidanta. Ita ba ta damu ba ko a wajen aikinta za ta iya faɗa wa maza sirrin gidanta da ma ƙawaye wannan ba gudunmowar komai . Ko zaman asibiti ko na Napep ya haɗa ta da mace za ta iya kwance mata sirrin gidanta kaf. Haka ko iyayenta sirrinsu bai tsira ba. Za ta iya kwashewa ta gaya wa mijinta.

Yar ƙarya/ fafa: Wannan ita ce mace mai burga kuma mai buri. Kashe kuɗinta ya fi samunta ko na mijinta yawa. Wannan mace ana mata laqabi da ɗiyar sarki a cikin talaka. Domin galibinsu iyayensu ko mazajensu ba masu hali ba ne. Amma idan ta yi wanka ta fito, kai ka ce ‘ya ko matar wani hamshaƙin ce. Ga kyautar bajinta kuma. ‘Yaruwa, ki ji tsoron Allah. Rayuwar ƙarya ba inda za ta kai miki.

Makira: Wannan ce mai fuska biyu ko zulwajahaini. Wacce abinda ke ranta daban, abinda take aikatawa daban. Wato Musa a baki, Fir’auna a zuci. Wannan mace ta zama sanadiyyar haɗa husuma da dama. Domin samun buqatar kanta da kanta. ‘Yaruwa ki guji haɗuwar ki da Allah, ki gyara halayenki.

Mai naci: Mace mai naci duk kyan halinta tana zama abar kyara musamman a wajen miji ko saurayi. A ɗabi’ar Ɗanadam yana buqatar a ba shi dama ya sha iska. Ba wai kullum ki dinga liqe masa ba. Ga damu da kiran waya ko saqon tes. Idan ba a amsa ba, ki yi ta fushi. ‘Yaruwa, ki ja ajinkinki. Ke mai daraja ce. Sai kin daraja kanki za a daraja ki. Haka, naci ba zai sa ki samu abinda Allah bai nufa ba. Ki bi a sannu.

Maha’inciya: Mace maha’inciya ita ce mai cin amanar mijinta a cikin dukiyarsa ko kuma neman wasu mazan a waje. ‘yaruwa ki ji tsoron Allah. Ko asirinki bai tonu a Duniya ba, akwai terere a lahira.

Mai son kanta: Mace mai son kanta ita ce mai fifita buƙatarta a kan ta kowa. Mijinta da kishiya da ‘yanuwanta har ma da ‘ya’yanta su suka fi cutuwa da wannan mugun hali nata. Ita buƙatarta ce sama da komai. Za ta iya saɓa wa kowa a kan ta samu ta biya. Idan ta biya kuma, ko waigen wani ba za ta yi ba. Ballantana ta san tasa buƙatar.

Mai zargi: Mace mai zargi ita ce wacce ba ta aminta da mijinta ko saurayinta. Kullum a cikin zargin suna ha’intarta take yi. Mata masu bincikar wayoyin mijinsu su ma suna cikin wannan rukuni. ‘Yaruwa kamata ya yi ki rabu da shi da Allah. Kuma ki yi masa addu’ar shiriya. Idan kika biyewa zargin nan, za ki jaza wa kanki ciwon hawan jini da makamantansa.

Mai bayyana adonta ga wanin mijinta: Akwai mata da yawa da ba sa yin ado a gidjensu sai idan za su fita unguwa. ‘Yaruwa ki sani, bayyana kwalliyarki ga wani bayan mijinki zunubi kawai kike jawo wa kanki. Garin neman gira ki zo ki rasa ido

Mara godiya mai ƙorafi: Wannan ita ce wacce ba ta gode wa Allah ballantana kuma ta gode wa mutane. Mace ce mara wadatar zuci ko kaɗan. Duk abinda ta samu, sai ta raina. Kawai ita burin wanda ya fi shi take yi. ‘Yaruwa ki bi a hankali. Dukkan abinda kike da shi, kika raina, to wani kamarsa yake nema bai samu ba. Wani ma rabi ko kwatansa yake nema. A rage buri sai a samu salamar zuciya.

Mai ƙarfa-ƙarfa: Ita ce macen da ba ta juyuwa ko kaɗan. Hasali ma ita take Fatan ganin ta juya mutane. Ko cikin ƙawaye ta fi son a ce ita ce tauraruwa wacce take faɗa a ji.

Tana matuƙar son biyayya amma sam ita ba ta iya yin biyayya. ‘Yar uwa me ya yi zafi? Ki sasaauta burinki ke ba komai ba ce face ‘yar adam wacce Allah zai kariɓi ran abarsa duk lokacin da ya so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *