Waƙa a wurina gado ce, inji Hajara Idris

“Sanadin soyayya na fara waƙa”

“Harkar fim aba ce mai kyau, sai dai ga waɗanda suka ɓata ta”

DAGA ABBA MUHAMMAD

Hajara Idris, wadda aka fi sani da Hajjo a masana’antar waƙoƙi da finafinan Hausa, sabuwar mawaƙiya ce kuma jaruma. Domin bata jima da bayyana a masana’antar, duk da ta daɗe da fara waka. Hajjo dai ɗiya ce ga fitaccen mawaƙin asharallen nan da ke zaune a Kaduna, wato marigayi Idi Moris, kuma ita ce babbar ‘yarsa. Hajara yarinya ce son kowa ƙin wanda ya rasa. Haka kuma ba ta da girman kai, ba ta da ƙin mutane, ga ta da fara da haba-haba da jama’a. Hajjo dai mawaƙiya ce kuma jaruma. Wannan ya sa wakilinmu ya zanta da ita domin jin ta bakinta game da yadda ta shigo harkar. Jarumar ta bada haɗin kai wurin amsa dukkan tambayoyin da aka yi mata. Ga yadda hirar ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Ki faɗa wa masu karatu cikakken sunanki da tarihin rayuwarki a taƙaice?
HAJARA: Ni sunana Hajara Idris, wato Hajara Idi Moris, wadda aka fi sani da Hajjo. Ni haifaffiyar Tudun Wada ce, an haife ni a shekarar 1992. Na yi firamare a Abubakar Mahmud Gumi a Tudun Wada, sannan na yi sakandare na a Shehu Abdullahi Gwandu. Na fara waka tun Ina ƙanƙanuwa.

Me ya ja hankalinki har ki ka fara waƙa?
Gaskiya ni ba zan iya cewa waƙa ba ta yi min rana ba, domin kuwa tun Ina ƙarama na ci arziƙin waƙa, mahaifina mawaƙi ne, amma na gargajiya. Saboda a garin Kaduna da kewaye ko ƙaramin yaro ka faɗa wa sunan mahaifina zai ce maka ya san shi, ko bai taɓa ganin sa ba, zai san sunansa.

To, dalilin haka, ka san an ce wani ka na iya gado, wani kuma haye ya ke yi. Sanadiyar haka zan iya haɗa abu a makaranta Ina buga tebur ni ce mawaƙiyarsu, wannan shi ya ja ra’ayina na fara son waƙa.

Kenan gadon waƙa ki ka yi?

Sosai kuwa gadon waƙa na yi, waƙa a wurina gado ce, kuma Ina alfahari da haka.

Ki na yin waƙoƙin gargajiya irin na mahaifinki ko kuma na zamani kawai ki ke yi?
E, ina iya yin waƙoƙin gargajiya da mahaifina ke yi, amma da yake ni mace ce, kuma an san cewa wancan na gargajiya ne maza kawai ke yi, ban taɓa ganin mace ta na yin irin wannan waƙar ba, shi ya sa ni ma ban maida hankali Ina yi ba, sai na maida hankalina a kan na sitidiyo.

Wane lokaci ne ki ka fara waƙa?
Gaskiya na fara waƙa ban wuce shekara goma sha biyar ba a lokacin. Saboda ba zan taɓa mantawa ba Allah Ya jiƙan mahaifina a lokacin yana nuna min kada in yi waƙa saboda ni mace ce ƙarama, in bari sai na mallaki hankalin kaina, kada in zo in samu wani abin duniya ya sa bazan yi sha’awar aure ba ko kuma ba zan iya kyautatawa iyayena ba, ko in kasa yi masu biyayya ba.

A lokacin Ina ɗan yi a voye, in na dawo gida aka tambaye ni daga ina ki ke, idan na ce, daga sitidiyo na ke, sai a yi min faɗa da cewa, in kiyaye duk abinda zan yi in yi tsakani da Allah. Ina jin daɗin addu’ar da mahaifina yake yi min. Ka ga wasu iyayen su matsawa ‘ya’yansu, kuma wannan matsawar ba shi zai sa su ji tsoron su ba, nasiha shi ne mafita.

Ni mahaifina yana yi min nasiha sosai, a ko da yaushe maganar sa in ji tsoron Allah, ni ba na ganin ki, amma Allah na ganin ki a duk inda ki ke, wannan nasihar na yi min tasiri sosai a cikin zuciyata. To tun a lokacin na fara waƙa, kuma na fara waƙa ne sanadiyyar soyayya.

Ko za ki iya faɗa mana wasu daga cikin waƙoƙinki?

Akwai waƙar ‘Share Hawaye’, ‘Masoyina’, akwai kuma wata waƙa da na yi mai suna ‘Ɗangata’, da sauransu.

Idan mu ka koma ɓangaren fim kuma fa. Ki na fitowa a fim?

Alhamdu lillahi. Ka san an ce da wani sanadin ka ke samun wani. Yanayin rayuwa da kuma zama da kowa lafiya, ta dalilin wani da ka ke ganin mutuncinsa, zai sa ka yi wani abin da ba ka yi tsammani ba. Da farko na fara fitowa ne a waƙoƙi, idan mutum zai yi bidiyon waƙarsa, sai ya kira ni mu yi tare.

To, daga haka sai abin ya ja ra’ayi na in fara fitowa a fim, saboda hakan yana da muhimmanci a wuri na, don na san harkar fim abu mai kyau ne, sai dai in kai ka ke so ka ɓata harkar ka.

Zuwa yanzu kin fito a finafinai kamar nawa?
Gaskiya ba su da yawa, don ba su wuce uku zuwa huɗu ba.A cikin su akwai ‘Kaico Na’, akwai ‘Sanadi’, na manta sauran gaskiya.

Ki na da ubangida?
E to, ba zan iya cewa kai tsaye ga wane shi ne ubangida na ba. Amma dai na san an tallafa min sosai gaskiya, an kuma taimake ni da kuma ba ni shawarwari idan na yi abin da ba daidai ba.

Ki na da kamfani na ki na kan ki ne ko kuma ki na da wani kamfani da ki ke zama ƙarƙashin sa?
Ni ba ni da kamfani na kai na, amma Ina zama a kamfanin Wassh Production. Ina ƙarƙashin wannan kamfani, kuma da shi na dogara.

Ya mu’amalarki ta ke da sauran ‘yan matan?
Ka san ana cewa duk wanda ya zauna lafiya a rayuwa shi ya so, kuma zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Ina da kyakkyawar alaƙa da su, saboda Ina ɗaukar kowa a matsayin ɗan’uwana, kuma in na yi abin da ba daidai ba, Ina so a gyara min, haka nima idan na ga ka yi ba daidai ba, in Ina da dama zan kira ka ni da kaina in faɗa maka ka yi ba daidai ba. Amma kuma in na gama zan baka haƙuri in na yi ba daidai ba.

Da wani fitaccen jarumi ki ke so ki ga kin yi aiki da shi?
Ba ni da wani jarumi da na ke so in yi aiki da shi, ni duk ɗaya na ɗauke su, ko wani jarumi da ka ga ni Allah ne Ya ɗaga shi, duk wanda Allah Ya haɗa ni da shi Ina maraba da zuwansa.

A ɓangaren mawaƙa kuma fa, kin tava waƙa da wani fitaccen mawaƙi?
E to, wanda na ke yin waƙa da shi ya fita, amma ka san halin rayuwa. Da Ɗayyabu D. Y na ke waƙa, domin a sitidiyonsa na ke waƙoƙina.

Menene burinki a kan wannan harka?
Burina shi ne, Allah Ya sa min albarka a cikin kasuwancina da sana’ata, domin ni sana’ata Ina alfahari da ita. Sannan Ina roƙon Allah Ya sa alkhairin da ban samu ba a baya, in samu a gaba. Kuma Ina so in zama wata da ma sauran abokan sana’ata bakiɗaya, in sha Allah.

Kin taɓa aure?
Na taɓa aure.

Yanzu ga ki a cikin wannan masana’anta, kuma ki na son ki ɗaukaka a masana’antar. Idan miji ya zo a yanzu za ki bar harkar ki yi aure?
Ai ɗaukakar Allah ta fi ta kowa. Mu duk abinda aka ce Allah da Manzon sa magana ta ƙare. Ai Allah ne ya ce a yi aure, kuma za mu yi aure. Ɗaukakar Allah ta fi komai, in na samu ɗaukaka zan samu kuɗi kuma in yi suna a duniya, da in yi suna a duniya in kasa yin suna a lahira wane ka ga ya fiye min. Suna a lahira shi na ke nema. Idan Allah Ya sa na sa mu miji, kuma Ina da shi a hannuna zan zauna da zuciya ɗaya babu tunanin wani abu.

Bayan rasuwar mahaifinku, akwai wanda ya gaje shi a cikin ku?
Alhamdu lillahi. Ƙanina ya fara yi, amma bai fiye yin na gargajiya irin na mahaifinmu ba. Akwai wanda yake tare da shi Surajo Sanfal, kuma wannan soyayya ta faro ne tun yana yaro mahaifinmu yake son shi. Bayan rasuwar mahaifinmu akwai ɗan abin da ya faru wanda bai yi min daɗi ba, don a lokacin na yi fushi sosai, na yi kuka har na ke cewa me ya sa ni ba zan iya yin abin ba, sai kuma na duba cewa, ni mace ce wata rana za a iya goranta min, sannan wata rana zan je gidan wani. Amma dai ƙanena ya na yi, sai dai bai cika yin yanda babanmu yake yi ba, ya fi yin na fiyano. Amma in aka kira shi, irin wancan ɗin ma yana yi, kuma salon mahaifina ya ɗauka tsaf.

Amma kuma idan ki ka duba akwai irin su Barmani Choge, Uwani Zakirai da sauran su, mata ne kuma duk sun yi irin wannan harka, kuma sun yi suna a duniya. Baki ganin cewa idan ki ka ɗauki salon mahaifinki za a ga cewa kin ɗauko sabon salo da ba a saba gani ba a wannan zamani?
Gaskiya haka ne, Ina yawan tunanin haka. Amma ni na fi so in yi aure ne, don mahaifina ya rasu da burin haka.

A ƙarshe wacce shawara za ki ba abokan sana’arki?
Shawara ta guda ɗaya ce, duk inda babba yake ya ja ƙarami a jiki. Akwai abubwan da ke faruwa da mu mawaƙa, idan Allah Ya baka dama ka tashi, idan ƙarami ya zo sai a riƙa nuna bai isa ba. Alhali baiwar da Allah Ya ba babban, shi ƙaramin yana da shi. Kuma mutane da yawa akwai abin da ke faruwa ba ma ga mu mawaƙa ba kawai, a lokacin da mutum yake tashe za ka ga an fi son waƙarsa, ka ga wannan na Allah ne. Ya kamata a ce duk lokacin da mutum ya yi waƙa in da gyara a ciki wani babban mawaƙin zai iya kiran sa ya gyara masa ba laifi ba ne. Sannan mutane ya kamata su amshi waƙar, saboda su ne jagora, su za su fidda ta duniya ta san ta. Don haka Ina roƙon na samanmu su riƙa Ɗaura mu a kan daidai.

Madalla. Mun gode.
Ni ma na gode.