Wa’adin 1 ga Disamba: NLC ta shirya yajin aiki a Zamfara, Katsina da Kuros Ribas bayan jihohi 33 sun ƙaddamar da mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO A. BABAJI

A halin yanzu, sauran jihohin da ba su kai ga ƙaddamar da biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na N70,000 suna ƙoƙarin ganin sun sun shiga sahun waɗanda suka fara biya, yayin da ƙungiyar ƙwadago NLC ta ce babu ja da baya game da wa’adin 1 ga watan Disamba da ta ba su.

Jihohi da ba su kai ga fara biya ba sune; Katsina da Kuros Ribas da kuma Zamfara wanda hakan ya nuna cewa sauran jihohi 33 da Abuja sun sun fara aiki da dokar albashi ta 2024.

Jihohi da dama ne suke biyan sama da N70,000 inda Legas da Ribas ke kan gaba da N85,000.

Ma’aikata a jihohin Akwa Ibom, Enugu, Oyo da Neja za su riƙa amfani da ƙarancin N80,000 yayin da Delta da Ogun sukai amince da N77,000.

Ebonyi, Osun, Benue da Kebbi kuma sun amince da N75,000; Ondo, N73,000; Kogi da Kaduna, N72,000; sai Kano da Gombe, N71,000.