Wa’adin tsofaffin takardun Naira: Mulkin mallaka biyan bashi da ɗakin kishiya

Daga LARABI LARABIN

Wadannan mutanen me suke nufi ne? Suna nufin mutane mutuwa za su yi a kan wannan canjin kuɗin da har yanzu bai shiga hannun talakawan ƙasar ba?

Ban san wata ƙasa ta banza a duniya sama da Nijeriyar mulkin Manjo Buhari ba.

Sanda aka canja Dala daga fara zuwa koriya, har lokacin Corona 2020, ana kashe farar.

Haka Riyal na Saudiya an canja shi sama da shekara biyar, kuma ana amfani da tsohon.

Kuɗin CFA na ƙasashe 11 ko 9 na Afirka da ake amfani da shi, an canja ƙananan daga kan Dala ɗari zuwa Samfuran (Wato fari ɗaya) amma har zuwa wajen 2019 dana daina zuwa ƙasashen ana kashewa. Ban sani ba ko har yanzu ana cigaba ko sun ɓata.

Yadda suke yi, an yi sabo to za a cigaba da amfani da su har sai lokacin da tsohon ya vata a hannun mutane, sabon ya wadata.

Amma ba haka abin yake ba a mulkin mallaka na Manjo Buhari ba.

Wannan rashin lissafin shi ne ya sa tun a wancan mulkin nasa na 1984 zuwa 85. International Monetary Funds (IMF): tare da Bankin Duniya suka soke kuɗin Nijeriya daga cikin kuɗin ƙasashen Duniya da za a iya fita da su wata ƙasar don yin kasuwanci kamar yadda yake kafin lokacin da Shugaba Buhari ya yi wancan canjin.

Kafin wancan canjin, mutum idan zai tafi duk wata qasa a duniya, ba ya buƙatar canja Naira zuwa Dala ko Yuro ko Fam. Kawai zai ɗauki Naira ne duk ƙasar da ya je zai canjar a can zuwa kuɗin ƙasar.

Amma daga lokacin da Buhari ya yi canjin kuɗin a wancan lokacin ya kuma ƙayyade lokacin daina karva irin wannan lokacin.

Shikenan ya jefa da yawan mutane cikin asara musamman waɗanda suke harkar canji a ƙasashen ƙetare. Saboda sun tara Naira, kuma ba su da hanyar da za su dauko kuɗin su kawo Nijeriya. Ko sun kawo ma, ba su da asusun ajiya a banki.

Sannan a wancan lokacin, bankuna ba su yawaita ba kamar yanzu. Shi ya sa sai ka fita tun safe har dare ba ka samu damar shigar da kuɗaɗenka ba.

Sannan a wancan lokacin, akwai ƙa’ida da aka bayar na iyakacin kuɗin da za ka iya shigarwa banki. Lokacin kuma babu fasaha ta aikin bankin kamar yanzu. Babu tiransifa, babu katin ATM, Wannan shi ya haifar da muguwar Asara hatta ga ‘yan Nijeriya.

Alhaji Larabi Larabeen (UNCLE LARABI), marubuci ne, kuma ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto ne daga Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *