Wacce rawa Ma’aikatar Jinƙai ta taka wajen magance talauci da zaman banza?

Duk da rahoton binciken da aka samo kwana-kwanan nan daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa  (NBS) cewa, sama da ‘yan Nijeriya miliyan 133 ne suke rayuwa cikin talauci, amma Ma’aikatar Jinqai da Agaji tana cigaba da jajircewa akan ƙudurinta na tsamo matasa daga ƙangin talauci da rashin aikin yi.

Ma’aikatar tana gudanar da ƙoƙarin nata ne ta hanyar Shirin N-Knowledge da shirin raya al’umma (NSIP) da sauran horarwa daban-daban.

Rahoton na Hukumar NBS cewar mutane sama da miliyan 133 ne a Nijeriya suke fama da talauci ya zama kamar wani ƙarin ƙaimi a wajen ma’aikatar ta jinƙai kuma ya zaburar da ita don yin aiki ba dare ba rana don ceto ‘yan Nijeriya daga talauci. 

Tun a shekarar 2019 da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro da ma’aikatar ta jin ƙai (FMHADMSD), ya ba da cikakken iko ga ministar ma’aikatar ta farko wato, Hajiya Sadiya Umar Farouq, da ta yi dukkan abinda za ta yi don tsamo ‘yan Nijeriya daga talauci. 

Da ma dai tun a shekarar 2016, gwamnatin ta Buhari ta ƙirƙiro da shirin (NSIP), wanda ofishin mataimakin shugaban  ƙasa Yemi Osinbajo yake kula da shi, daga bisani kuma aka ƙirƙiro FMHADMSD a shekarar 2019, wacce ta cigaba da shugabantar  NSIP, da sauran shirye-shiryen da suka shafi magance talauci, rashin abin yi da rashin tsaro ta hanyar sanar da abubuwan yi. 

Shirin N-Power yana daga cikin shirye-shiryen da suke ƙarƙashin NSIP, wanda an yi shi ne saboda matasan Nijeriya masu digiri da marasa digiri waɗanda suke a tsakanin rukunin shekaru na 18-35 kuma ana biyan masu digiri Naira 30, 000, su kuma marasa digiri, Naira10, 000 kowanne wata har sai sun kammala shirin nasu. 

Shirin N-Power shiri ne da ya haɗe kowa da kowa kuma ya mai da hankali kacokan ga ‘yan Nijeriya marasa abin yi. Domin ya sa su samu hanyar da za su dogara da kansu. 

Shirin N-Knowledge wanda ya horas da mutane 7,000:

A dai ƙoƙarinta na ganin ta magance talauci, rashin aikin yi da sauran matsaloli, ma’aikatar jin qai ta horas da mutane 7,000 a zagaye na biyu na rukuni na C  a shirin N-Knowledge a faxin shiyyoyin ƙasar nan guda 6.

A yayin da take jawabinta a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata, 15 ga Disambar 2022, a yayin taron rufe horaswar da aka yi wa ‘yan shiyyar Arewa ta tsakiya, Hajia Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa, wannan horaswar wata ‘yar manuniya ce wacce take nuna irin dagewar ma’aikatar wajen ƙoƙarin magance zaman kashe wando. Wanda a cewar ta hakan yana ɗaya daga cikin manufodin shugaba Buhari na gina matasa tare da rage zafin talauci a Nijeriya.

A cewar ta: “Ina matuƙar farin cikin yaye  waɗannan daliban horaswa na N-Knowledge na shiyyoyin ƙasar nan guda 6. Ya kamata a san cewa, wannan abinda yake faruwa a nan Abuja a yau yana faruwa ma a cibiyoyin horaswa guda 11 a faɗin shiyyoyi 6 na ƙasar nan, a inda ake horas da ɗalibai 7,000 waɗanda aka samu nasarar horas da su a shirin N-Knowledge zagaye na biyu a rukuni na C, inji ta”.

Ministar ta ƙara da cewa, NSIP ɗaya ne daga cikin shirye-shiryen da suke masu girman gaske. Wanda a duk shekara ake zuba masa Dalar Amurka biliyan guda domin a inganta rayuwar marasa galihu da matalauta a ƙasar. Hakazalika a cewar ta, shirin N-Power shi ma yana daga shirye-shiryen da ya yi tasiri matuqa a cikin rayuwar matasa marasa galihu a Nijeriya, har ma da mutane masu naƙasa.   

A cewar ta, shirin N- Knowledge wani shirin koyon sana’a ne da ake gudanar da shi na tsahon watannin 9. Wato watanni 3 na horaswa, watanni 6 kuma na koyon sanin makamar aiki. Kuma ana koyar da sana’o’i da dabarun neman kuɗin kala-kala da suka shafi harkokin kanikanci da fasaha na kwamfuta da sauransu. Kuma gwamnati ta yi wa kowanne ɗaya daga cikin ɗaliban tanadi ta hanyar samar musu dukkan kayan aikin da suke buƙata don gudanar da sana’o’in da suke koya don samar musu da ƙwarewa. Kuma ta tanadar musu alawus na wata-wata na 10,000.

A ƙarshe Ministar ta bayyana cewa, tana fatan su ɗaliban koyon sana’ar su gane irin sa’ar da suka yi suka kasance zaɓaɓɓun matasan Nijeriya masu fasaha da suka zama wani vangare na wannan horaswar. 

Shi ma a nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar jin ƙai Dakta Nasiru Sani Gwarzo, ya bayyana cewa, wannan shiri ba ƙaramin shiri ba ne. Domin  an yi ƙoƙarin wajen horas da matasa yadda ya kamata domin tunkarar ayyukan da suke gabansu na miƙewa su tsaya da ƙafafunsu. 

Dakta Gwarzo ya ƙara da cewa, kamar yadda aka sani, shirin N-Power shiri ne na musamman da gwamnatin Buhari-Osinbajo ta samar don taimaka wa matasa ‘yan shekara 18 zuwa 35 marasa aikin yi, su ma su samu abin yi. Kuma shiri ne da ya haɗa kowa da kowa. 

Sannan ya bayyana godiyarsa ga ministar jin qai Hajiya Sadiya Umar Farooq a kan wannan shiri da ta samar na N-Knowledge wanda aka gudanar da horaswa ga mutane a fadin shiyyoyi Nijeriya guda 6. 

Ya ce tabbas waɗannan ɗaliban koyon sana’ar da ake yayewa a yau Alhamis 15 ga Disamba, 2022 sun samu horaswa ingantacciyar mai kyau. Kuma yana fatan za su yi amfani da wannan dama da kuma abinda suka koya a inda ya kamata.

Domin zai taimake su a rayuwa matuƙa. 
“Zan so na ƙara jaddada cewa ya kamata dukkan masu amsar horaswar su kalli wannan dama a matsayin rahama a gare su wacce ba za su yi wasa da ita ba. Domin sun yi mu’amala da mutane iri daban-daban, sun yi abokai da suka yi koyo tare da sauran abubuwan da suka koya. Sai ku sanya waɗannan abubuwa da kuka koya a gaba ku gyara gobenku. Ku tuna da cewa, mutane da dama sun nemi wannan dama amma ku ne kuka samu damar haye zaɓen da aka yi na waɗanda suka dace. Don haka ya kamata ku ɗauki abin da muhimmanci”. Inji shi.

Waɗanda suka amfani sun yaba wa ministar jin ƙai:

A yayin da suke yabawa ga Ma’aikatar jin-ƙai, da yawa daga waɗanda suka amfani da shirin N-Knowledge sun ce za su yi amfani da abinda suka koya a wannan shirin don cicciɓa kansu su fita daga talauci sannan kuma sun yi kira ga takwarorinsu da su ma kada su yi wasa da wannan ilimi da suka samu daga masu koyar da su a wannan shirin.

Ɗaya daga cikin waxanda suka amfana, Khadija Abdulrahman Yunus, daga Jihar Filato ta bayyana cewa, wannan shiri ta rabauta da shi sosai domin ta karanta kimiyyar kwamfuta amma ba ta samu sararin gwada sana’ar ido-da-ido ba sai yanzu.  

Ta qara da cewa, an rarraba musu kayan aiki waɗanda za su iya amfani da su don yin gyaran kwamfutoci da manya da ƙanana da wayoyi samfurin daban-daban. Ta ce wannan shirin ba ƙaramin taimaka musu ya yi ba. 

Daga ƙarshe ta yi kira ga takwarorinsu da su san cewa, wannan ba shi ne ƙarshe ba. Su cigaba da adana kayan aikinsu suna yin aiki da su a duk sanda buƙatar hakan ta taso. 

Sannan kuma akwai wani mai suna  Ogenyi Isaac, daga jihar Biniwai wanda ya yi alƙawarin zai yi amfani da wannan ilimi da kayan aiki don kafa sana’ar gyaran waya da kwamfutoci da sauransu. 

Daga ƙarshe ya gode wa mai girma ministar ma’aikatar jin ƙai a kan wannan dama da aka ba shi ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka amshi wannan horo. Kuma ya yi alƙawarin amfani da kuɗin alawus-alawus ɗin da ya samu a aikin wajen kafa sana’arsa. Kuma ya yi kira da sauran takwarorinsu da su aikata haka su ma.