Wahalar rayuwa ta sa wata mata jefa ‘ya’yanta cikin rijiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata mata a da ke zaune a yankin Ibuaje, Osogbo, Babban Birnin Jihar Osun ta tsunduma ‘ya’yanta mata guda biyu cikin rijiya.

Mazauna yankin da matar take sun ce dama matar ta sha yin ƙorafi akan yadda take ɗanɗana wahalhalun rayuwa da kuma ɗawainiya da waɗannan ‘ya’ya.

Wani mazaunin unguwar da yake bayyana yadda abun ya faru, ya ce “Matar ta fara jefa babbar yarinyar ne mai kimanin shekara bakwai da haihuwa cikin rijiyar, sai kuma daga bisani ta jefa ƙaramar ‘yar kimanin shekara biyar, da misalin ƙarfe biyu na rana.”

Ko a lokacin da ake haɗa wannan rahoto, yaran suna cikin rijiyar, inda ma’aikatan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun suke ƙoƙarin ceto su.

Da yake bayyana wa manema labarai halin da ake ciki, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun, Mista Ibrahim Adekunle ya ce rijiyar tana da gaba 24 kuma maƙare take da ruwa a cikinta.

Ya ce ma’aikatan hukumar kashe gobara sun yi iyakacin ƙoƙarin su wajen ceto rayuwar yaran.

Da take magana cikin wani yanayi, mahaifiyar yaran ta ce a da tana zaune ne a ƙasar waje kafin daga bisani ta dawo ƙasar nan, inda ta bayyana cewa irin wahalhalun da ke a Nijeriyar ne ya sa ta aikata hakan.

To sai dai kuma wasu mazauna yankin da take sun ce akwai yiwuwar matar ta samu taɓin hankali bayan dawowar ta Nijeriya.