Wai sai an sace kowa ne?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya rahotanni da su ka shafi sace mutane har gida na tada hankalin jama’a kuma kusan kullum sai irin wannan labari ya fito. Kamar yadda in mutum ya hau yanar gizo zai ga batun ta’aziyya kullum wane ko wance sun rasu, hakanan kan sace mutane ya ke. A farko lamarin an faruwa ne kan hanyar daji mai duhun bishiyoyi har ya dawo wasu dazuka ko ma anguwannin daf da cikin gari.

Misalin hakan shi ne yankin kamfanin Olam da ke kusa da shiga birnin Kaduna. Da dama-dama idan ma miyagun irin sace mutum su ka yi da shiga daji su na bugo waya don neman kuɗin fansa, amma mafi mugunta su ne waɗanda su ka kashe mutane a gida ko a daji. Mun samu labarin irin wannan juyayi na shiga gidan direban jirgin sama Abdulkarim wanda ɗan sanata Bala Ibnu na Allah ne a Kaduna. Ko ma su waye miyagun masu sata ne, ‘yan fashi ne ko masu kisan gilla ne sun aikata wannan mugun aiki na kisan gilla ga wannan bawan Allah. Zubar da jinin mutum shi ne mafi munin laifi a duniya. Ba wani laifi da mutum zai yi ga ɗan adam ya wuce kimar kwatance da ya wuce zubar da jinin mutum.

Baya ga yadda illar ta sacewa da rasa rai daga miyagu ya yi yawa a Kaduna, hakanan ya shiga Katsina. Babban labarin da mu ka samu na abun juyayi na sace mutane da farautar su kamar bisashe ya zama abun takaici aiunun da jiya wajajen da a baya lami lafiya su ke zaune ba rani ba damuna.

Wasu mutanen a kan shiga har gidajen su a sace su. Wasu sai an yi abun ashsha da su ko da mutan gidan su da hakan manuniya ce ta miyagun ba wai kuɗi kaɗai su ke nema ba, a’a akwai cusa bakin cikin dindindin ga jama’a ta hanyar cin zarafin matan su ko ‘ya’yan su.

Fakewa da cewa ramuwar gayya ce ko a baya an cutar da wasun su ne su ke aikata haka don ba wata sana’a da za su yi ba zai taba zama hujjar yin fyaɗe ko gaggawar buɗe wuta ba. Za a iya amincewa da mai neman kuɗin fansa na da dama-dama kan wanda zai haɗa dukkan zunuban uku ya sace mutane, ya nemi kuxin fansa sannan ya yi fyaɗe ga mata ko kuma mafi muni ya yi kisa. Haƙiƙa ko ba a ce akwai illar shan ƙwaya ko kamru uwar laifi a wannan lamari ba, a fili ya ke masu aikata miyagun aiyukan a buge su ke wa imma da kayan maye ko kuma a buge su ke da giyar rashin imani.

A addinance ma akwai laifukan da kafin mutum ya aikata su, sai an zare ma sa imani ya zama ba ya tsoron sakamakon da zai tarar a wajen ubangijin talikkai. Kullum a na mutuwa da hakan in bai zama darasi da zai sa mutum nadama ko daina mugun aiki ba, to gaskiya zuciyar sa ba ɗigon rahama kuma ta kan yiwu ya na daga abun da malaman fikihu ke cewa alama ce ta taɓewa da toshewar basira. Duk wanda ya taɓa kuma basirarsa ta toshe to a gaskiya ba ma amfanin zama kusa da shi. Yo ina amfanin zama a kusa da marar arziki a duniya kuma sai yadda hali ya yi a lahira?

Varayin sun sace tsohon daraktan hukumar kula da kafafen rediyo da talabijin na Nijeriya NBC shiyyar Borno Ahmed Abdulkadir da ya ƙara shahara a duniya bayan ya yi ritaya daga aiki da hakan ba mamaki ya sama ma sa wadataccen lokaci na bayyana a kai a kai a yanar gizo da ba da labaran muhimman abubuwan da ya kan gudanar yau da kullum. Duk wanda su ka san shi za su fahimci mai ƙaunar ba da labarin duk wani abun alheri da ta shafe iyalin sa kama daga matan sa biyu zuwa ‘ya’yan sa ciki kuwa har da likita.

An sace Ahmed da ‘yarsa a gidansa da ke Bakori a Katsina.

Labarin ya fito ta shafin babban edita a jaridar Blueprint Ibrahim Sheme.

Tuni aka taƙarƙare da addu’a a shafukan abokai da dama a yanar gizo don fatar kuɓutar Abdulkadir da ‘yar ta sa daga hannun ɓarayin da ke addabar jihar Katsina.

A yanzu haka dai jami’an tsaro su na kai hare-hare a mavoyar ɓarayin a jihar Zamfara bayan kashe layukan sadarwa na waya. Shawarar da na ga wasu masu sharhi na bayarwa ita ce ta yin takatsantsan don ka da ruwan wuta da a ka ce a na yi ya shafi wa imma waɗanda a ka sace ko kuma waɗanda ka iya taka ƙafar ɓarawo. Don haka wannan farmaki na buqatar juriya da yin aiki cikin haɗiye fushi da yin amfani da dabarun kwance damarar yaƙi don samun nasara mai ɗorewa.

Duk da ba cikeken bayani kan yadda yaqi da ɓarayin ke kasancewa daga wajen hukuma, hakan ta sa mutan yanar gizo yaɗa bayanai da ba su cika labarin da sahihan kafafen labaru za su riƙa dogara da su ba. Mafiya hankalin mutan yanar gizo su ne masu fatar alheri da dakarun Nijeriya don cimma muradin wannan farmaki duk da kuncin da ya ke tattare da shi na rufe layin waya, dakatar da hada-hadar fetur a jarka, hana cin kasuwar dabbobi da sauran su. Koma wani kunci za a shiga indai kwalliya za ta iya biyan kuxin sabulu dai a cigaba da godiya ga Allah da fatar samun nasara don amfanin dukkan al’ummar Nijeriya masu kaunar zaman salama ba kare bin damo.

Daidai rubuta wannan shafi sai ga labarin sace sarki sukutum kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ido na ganin ido! Rahoto na bayyana cewa varayi sun sace Sarkin Bungudu a jihar Zamfara Alhaji Hassan Attahiru a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Varayin sun buxe wuta kan kwambar motocin Sarkin mai daraja ta ɗaya inda jami’an tsaron sa su ka maida wuta amma varayin su ka ci galaba kan su inda su ka tafi da Sarkin zuwa tungar su a daji. Mai martaba ya baro miyagun iri a jihar ƙaddara ta sake haɗa shi da wasu a kan hanya.

Kusan a lokaci guda miyagun iri da ke addabar masarautar Zazzau sun buɗe wuta inda su ka ji wa wani soja raunuka da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa daga bisani. Bisa ga rahoton da mu ka samu akasin ya auku a Milgoma da ke ɗaura da asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.

Kazalika miyagun sun sace wata mata da ‘ya’yan ta.

Labarin ya nuna miyagun su kimanin 30 da makamai sun buɗe wuta yayin da jami’an tsaro su ka garzayo wajen don kawo xauki amma su ka samu hanyar tafiya da matar da kuma ji wa sojan rauni.

A kwanakin baya Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Bamalli ya koka cewa ɓarayi sun addabi masarautarsa.