Waiwaye: Tsofaffin mawaƙan Hausa da suka kafa tarihi (1)

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda muka sani, waƙa da kiɗa wata ɗabi’a ce da ke da muhallin zama a zukatan fiye da rabin kason mutanen da ke rayuwa a doron ƙasa, wannan ta sa a cikin kowacce alƙarya za ka tarar da kiɗa da waƙa a layin farko-farko na ababen da suke da muhimmanci gare su.

Wataƙila wannan ne dalilin da ya sa ake yawan samun ƙaruwa a duniyar waƙa da kiɗa, duk da cewa ba kowa ba ne daga cikin waɗanda suka shiga harkar suke samun karɓuwa ba.

A tawa fahimta, waƙa baiwa ce da ake yin kyautarta ga wanda mahaliccin bayi ya ga dama, tamkar dai rubutu da sauran ababe da ya shafi ƙirƙira, don haka ba kowa ne zai shiga ya samu karɓuwa ba. Duk da cewa, wasu na ganin shuhura ta ɓangaren waƙa abu ne kawai na sa’a, idan ka shiga da ƙafar dama, sai harkar ta ɗaga ka sama, mutane su so duk abinda ka dama ka shayar da su. Da wannan suke ganin kowa ma zai iya yin waƙa, matuƙar ya samu limamin ƙwarai da ya ƙware sosai a ɓangaren, ya saka su a hanya yadda ya kamata.

Sai dai ba za a yi tafiya da nisa ba za a iya rushe wannan fahimtar tasu, duba da cewa, mawaƙa da dama sun taho, sun shuɗe, amma wasu daga ciki ne kawai duniya ta keɓe tana tunawa da su a matsayin gwanaye a ɓangaren.

Da wannan ne, jaridar Manhaja, ta ɗaura aniyyar kawo wa masu karatunmu, wasu daga cikin mawaƙan Hausa da suka taka muhimminyar rawa a duniyar waƙa. Da yawa daga cikinsu sun bar duniya, sai dai sun yi abinda duniyar ta kasa mantawa da su.

Dan Maraya Jos: 

(Dan aji ɗaya mai digiri)

Daya daga cikin mawaƙan da suka kafa tarihin da har yau ƙasar Hausa ke alfahari da shi, mawaƙin da ya nuna irin tasa gwanintar da ta zama sabon abu a lokacinsa ta hanyar zamanantar da waƙoƙain da malam Bahaushe ya riƙa a matsayin nasa. 

Wani abin burgewa game da mawaƙin, ya yi amfani da baiwar da yake da ita wurin faɗakarwa kan sha’anin neman ilimi, siyasa da makamatansu. Mawaƙin da bai taɓa shiga aji ba, amma sanadiyyar waƙa ya zama mai digiri, kuma ɗaya daga cikin mawaƙan gargajiya na farko da suka fara kaɗa jita.

Dan Marayan Jos, mawaƙin da ya samu shahara ba iya ƙasar Nijeriya ba, har ma da wasu ƙasashen Afrika, yayin da waƙoƙinsa har wa yau suke yawo a kunnuwan mutane. ɗaya daga cikin mawaƙn Hausa da Turawa suka yaba wa bajintarsu.

Haifaffen garin Jos, ta Jihar Filato ne. An haife shi a ranar 20 ga watan Disamba, shekarar 1946. 

Idan mun nutse kan bayyanin asalin mawaƙin, za mu iya cewa, waƙa a wurinsa ba tsinta ya yi a ƙasa ba, domin ya fito daga tsatson mawaƙa, don haka ya yi wa kiɗa da waƙa sammako, wannan ne ya ba shi damar koyar kaɗa kayan kiɗa da dama daga wurin kakanshi, kamar kuwaru, gurmi da sauransu.

Allah Ya ɗauki ran mawaƙi ɗan Maraya a ranar 20 ga watan Yuni, shakarar 2015, a garin Jos. Ya mutu yana da shekaru 68. 

Dan Maraya ya yi waƙoƙi da dama da har yau ana saka su a gidajen rediyo da wuraren taruka, sakamakon tasirin da suke da a wannan zamani da muke ciki, kamar waƙar ‘Teacher Uban Karatu’, ‘ɗan Adam mai Wuyar Gane Hali’, ‘Lebura’, da sauransu.

Amina Rawaram: 

(Mai muryar zinare)

Bai zama abin mamaki ba idan sunan Amina Rawaram bai zama sananne a tsakanin masu tasowa a wannan zamani ba, kasancewarta Kanuri da ta fito daga Maidugu, sai dai idan aka saki waƙoƙinta, da yawa za su gane su. Shuhurar ta ba ta tsaya a iya masu jin yaren nata ba kawai, domin tana da masoya da dama a cikin lungu da saƙon Nijeriya, duk da cewa, da yawansu ba su san abinda ta ke faɗa a waƙoƙin ba. 

Amina Rawaram ta kasance ɗaya daga cikin kaɗan na mawaƙan da aka azurta su da murya mai matuƙar tasiri ga masu sauraron ta. Tana kuma jerin matan da suka ƙaryata zancen nan da ake cewa, waɗanda aka ba wa murya mai matsananciyar daɗi ba su cika kyau sosai ba, dalilin kasancewarta kyakyawa da ke da dogn gashi.

A ɓangaren shuhura za mu iya cewa ba ta tsaya a iya gida Nijeriya ba, domin ta kai har a gidajen rediyon ƙetare amon muryarta na ta shi, kamar Chadi, Nijar, Sudan da sauransu.

Idan mun koma sashen mutanen ta, wato mutan Borno, zancen muhimmancinta da alfaharin da suke yi da ita ba zai misaltu ba, domin har hula sukutum suka raɗa wa sunanta, wadda ta samu karɓuwa ga manyan mutane da yawa.

Barmani Choge:  

(Idan ba ka san Barmani ba, ka tambaye mata)

Kusan zan iya cewa, a kusa, tun daga da har zuwa yanzu ba a taɓa mawaƙiyar ƙwarya da mata suka yi na’am da ita kamar Hajiya Sa’adatu Ahmad, wadda aka fi sani da Barmani Choge. Haifaffiyar garin Gwaigwayi, Jihar Katsina.

An haife ta a shekarar 1945, inda ta fito a tsatson malamai, don haka ta samu ginin ilimin addini mai ƙarfi. 

Kamar yadda tarihi ya sanar, Barmani Choge, ta soma da waƙa tun a zamanin ƙurciya, inda ta ke ‘yan waƙe-waƙe a wasannin dandali da suke fita.

A lokacin da ta ke ‘yar shekara 15 aka yi mata auren fari da wani ɗan kasuwa, wanda ya kasance uban ‘ya’yanta 12. Wannan auren da Hajiya Sa’adatu ta yi da mijinta Alhaji Aliyu ne ya zame mata tsani a harkar waƙa, domin kasancewar sa ɗan mawaƙa, don haka ya ƙarfafa mata gwiwa yayin cikar burinta a fagen waƙa. Da wannan ta fara zuwa taruka, musamman na aure tana waƙoƙin biki.

ɗaya daga cikin muhimman dalilan tasirin waƙon Barmani Choge ba zai rasa nasaba da irin waƙoƙin da ta ke yi ba, waɗanda suka shafi zaman aure da rayuwar mata bakiɗaya, inda sau da dama ba a rasa ‘yan ƙananin batsa, wadda ke ƙara wa abin armashi ga kaso mai yawa na masu sauraren waƙoƙin nata.

Idan ka saurari maƙoƙin mawaƙiya Barmani Choge da kunnen fahimta, za ka tarar da cewa, ba kawai nishaɗi ne tsagaro ba, suna ɗauke da darrusa masu yawa, musamman ga matan aure. Wannan ya sa waƙoƙin nata da suka tashi sama, suka yaɗu, kuma har yau da ba ta raye ba su sauko ba.

A shekarar 1991 ne Allah Ya yi wa mijin mawaƙiyar yasuwa, inda daga baya ta ƙara aure, wanda ya yi ƙarkon shekara ɗaya, kafin rabuwa ta zo. Daganan ta mayar da hankali sosai kan harkar waƙoƙinta, har kusa ga shekarunta na ƙarshe a duniya.

Hajiya Sa’adatu Ahmad, ta rasu a ranar 2 ga watan Maris, shekarar 2013. Ta rasu a garin Funtua, Jihar Katsina.