Waiya ya nemi masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a kafafen labarai su riƙa amfani da kalamai masu tsafta

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga masu gabatar da shirye-shiryen da suka shafi harkokin siyasa musamman a gidajen rediyo da su kiyaye amfani da kalmomi masu kyau a yayin shirye-shiryensu.

Waiya ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a gidajen rediyo ta kai masa ziyara a ofishinsa.

Ya ce, lallai akwai muhimmiyar rawa da za su riƙa takawa wajen ganin baƙinsu ba su furta kalmomi marasa kyau ba, waɗanda galibi su kan ƙunshi cin-fuska ko nuna rashin girmamawa ga wani ko wasu ɓangare.

Ya kuma tabbatar masu da cewa gwamnati za ta samar masu da wani shiri da zai taimaka wajen inganta ƙwarewar ayyukansu.

Waiya ya jaddada aniyar ma’aikatarsu ta bada tallafi ga walwalar ƙungiyar, don cigaba da yi wa al’umma hidima cikin yanayi mai gamsarwa.

Ya ƙara da cewa, haɗin kansu yana da muhimmanci wajen dakatar da yaɗa kalamai na zagi a yayin tattauna batutuwan siyasa.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar, Abdullahi Muhammad Wali ya ce, sun ziyarci Waiya ne don taya shi murnar naɗa shi kwamishina da gwamnatin jihar ta yi, ya na mai tabbatar masa da cewa za su yi iya baƙin ƙoƙarinsu wajen ganin an kawo ƙarshen amfani da munanan kalamai a yayin shirye-shiryen.