Wakilan ƙasashe masu tasowa daga Asiya da Afirka dake ofishin MƊD na birnin Geneva sun ziyarci Xinjiang

Daga CMG HAUSA

Bisa gayyatar da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta yi musu, wasu jakadun ƙasashe masu tasowa, daga ƙasashen Asiya da na Afirka dake aiki a ofishin MƊD na birnin Geneva, sun ziyarci jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta, dake Arewa maso yammacin ƙasar Sin.

Yayin ziyarar da jami’an suka gudanar tsakanin ranakun 24 zuwa 27 ga watan Agustan nan, sun tattauna kai tsaye, da ɗaliban da aka yaye daga cibiyoyin koyar da sana’o’i ta Xinjiang, da malaman addinin musulunci, da al’ummun ƙabilu daban daban dake jihar.

Bisa abubuwan da suka gani, wakilan su jinjinawa gwamnatin ƙasar Sin, bisa nasarorin da ta cimma a fannin daƙile ayyukan ta’addanci, da kare ‘yancin al’umma na gudanar da addini, da kare martabar al’adun kananan ƙabilu.

Jakadun sun kuma bayyana aniyar su ta goyawa ƙasar Sin baya, a yunƙurin ta na bayyana gaskiyar al’amari dangane da Xinjiang, da kawar da zarge zargen da wasu sassa ke yi don gane da yankin na Xinjiang.

Fassarawar Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *