Wakilin Sin a MƊD ya yi kira ga ƙasashen duniya da su haɗa kai don yaƙar kalaman nuna ƙiyayya

Daga CMG HAUSA

Jiya Litinin, zaunannen wakilin Sin dake MƊD Zhang Jun, ya yi jawabi a wajen kwarya-kwaryar taron MƊD game da ranar adawa da kalaman nuna kiyayya, inda ya yi kira ga ƙasashen duniya da su mutunta juna tare da yin shawarwari cikin adalci don yaƙi da irin wadannan kalamai.

Zhang Jun ya nuna cewa, ƙasar Sin na goyon bayan babban taron MƊD da ya kira irin wannan taro don tunawa da rana ta farko a wannan fanni. Babban taron MƊD ya zartas da kuduri a watan Yuli na shekarar 2021, inda aka mai da ranar 18 ga watan Yuni na ko wace shekara a matsayin ranar yaƙi da kalaman nuna kiyayya, Sin ta kasance ɗaya daga cikin kasashen da suka gabatar da wannan ƙuduri.

Zhang Jun ya nuna cewa, tinkara da kuma kawar da irin kalaman na buƙatar ƙasashe daban-daban su nace ga mutunta juna da yin shawarwari cikin zaman daidaito. Kamata ya yi wasu ƙasashe su yi tunani mai zurfi su dubi kansu tare da yin watsi da girman kai da nuna bambanci, da mutunta moriyar sauran ƙasashe.

Kada a yada kalaman nuna ƙiyayya da ma labarai na jabu ta hanyar fakewa da kare ‘yancin fadi albarkacin baki. Kuma ya kamata a yi haƙuri da juna da kara tuntubar juna da ingiza mu’ammalar al’umma da kawar da rashin fahimtar juna, matakan da za su kasance a matsayin tushen kawar da kalaman nuna kiyayya.

Mai Fassarawa: Amina Xu