Wakilin Sin ya buƙaci a ƙara ƙoƙarin taimakawa ƙasashen Afirka yaƙar ta’addanci

Daga CMG HAUSA

Zaunannen wakilin ƙasar Sin a Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), Zhang Jun, ya yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa, da su ƙara ba da taimako ga ƙasashen Afirka don ƙara ƙwarewarsu a fannin yaƙar ta’addanci, ta yadda za a kawar da matsalar daga tushe.

Jami’in Sin ya furta haka ne a taron manyan jami’an yaki da matsalar ta’addanci a nahiyar Afirka na kwamitin sulhu na MƊD, inda ya shawarci ƙasashe daban daban, da su taimakawa ƙasashen Afirka ƙarfafa ɓangarori masu rauni, da ba da karin tallafi na kuɗaɗe, da kayayyaki, da bayanai da dai sauransu.

Jami’in ya kuma nanata cewa, ya kamata a girmama ’yancin ƙasashe, da ɓangarorin ƙetare dake haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka, yayin da ake hadin kai da su wajen tinkarar matsalar ta’addanci, kana a daina gindaya musu wasu sharudda da suka shafi batun siyasa.

Zhang Jun ya ƙara da cewa, ya kamata MƊD ta ƙara mai da hankali kan ra’ayoyin ƙasashen Afirka, da buƙatunsu na raya ƙasa, da ƙoƙarin samar musu da yanayi mai kyau da zai taimaka musu wajen cimma burin da suke fatan cimmawa.

A cewar jami’in, a ko da yaushe ƙasar Sin ta kasance mai nuna goyon baya ga ƙasashen Afirka, wadda kuma ke samar musu da gudunmawa ga ƙoƙarinsu na tabbatar da kwanciyar hankali.

Ƙasar Sin za ta ci gaba da haɗa kai tare da gamayyar ƙasa da ƙasa, wajen samar da ƙarin taimako ga ƙasashen Afirka, don ganin an tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a nahiyar.

Mai fassara: Bello Wang