Walimar mahaddata 1,800 a Ma’assar Khallipha Isahaƙ Rabi’u cigaban Musulmi ne – Hajiya Aisha Hamdan     

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa samun ɗalibai 1800 da suka haddace Alƙur’ani mai girma a makarantar Mu’asasa da Sheikh Khallipha Isahaƙa Rabiu ya kafa da cewa babban cigaba ne kuma abin farin cike ne da godiya ga Allah, ɗaukacin al’ummar Musulmi duniya baki ɗaya, kamar dai yadda Hajiya Aisha Abdusamadu shugabar kamfanin gidan abinci na Hamdan ta bayyana a yayin walimar da aka gabatar a makon da ya gabata a Kano.                

Hajiya Aisha Hamdan wacce ɗaya ce daga cikin iyayen Hafizan 1800 da suka yi hadda, ta ce wannan makararanta ita ta yi tun tana ƙarama kuma yau ga shi ‘ya’yanta uku sun haddace Alƙur’ani mai girma a wannan Mu’asasa ta Khadimul ƙur’an.

Ta ce kafin wannan walima babban ɗanta namiji ya yi haddar, inda yau kuma ga Aisha Ahamad Isa da Khadija Ahamad Isa, su ma sun yi haddar. Ta ce wannan ni’ima ce ba ma daga garesu ba, har da ɗaukacin al’umma.

Hakazalika ta yi addu’ar Allah ya yawaita haka a tsakanin al’umma da irin ni’ima ta samun ilimi, inda kuma ta nemi iyaye su  tashi tsaye wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu kasancewar yara matasan yanzu su ne iyaye kuma shugabannin gobe.

A ƙarshe Hajiya Hamdan ta shawarci hukumomi da su taimaka wa fannin harkar ilimi kamar yadda Gwamnatin Kwankwaso da ta Abba, suke yi da suka ɗauki nauyin ‘ya’yan talakawa a gida da wajen ƙasar nan kuma akwai buƙatar al’ummar mu su zurfafa ilimin addini da na zamani kamar yadda  Musulmin Kudu maso yammacin Nijeriya suke yi.