Wanda ake tuhuma da kisa ya buƙaci alƙali ya ɗaura masa aure

Wani mutum da aka gurfanar a gaban kotu kan zargin aikata kisa ya buƙaci alƙalin da ke sauraron shari’ar ya ɗaura masa aure da masoyiyarsa ana tsaka da zaman kotu.

Ana tuhumar Kashwan Flower da harbe wani mutum a yankin New York na Jihar Pennsylvania da ke ƙasar Amurka ne.

Lauyan wanda ake tuhumar ɗin, Attoni Brian Perry, ne ya gabatar da buƙatar a gaban alƙalin kotun ranar Talata ana tsaka da zaman shari’ar, yana mai roqa masa alfarma alƙalin da ya ɗaura aurensa da masoyiyarsa a kotun bisa la’akari da cewa, masoyiyar tasa ba ta cikin waɗanda za su bayar da shaida a shari’ar.

Lauyan, bayan miqa buƙatar wanda ya ke ƙara, ya yi ƙarin bayani cewa wannan ne karo na farko da ya taɓa neman irin wannan alfarma.

Duk da cewa alaƙalin kotun ya amince da buƙatar, amma ya bada sharaɗin cewa har sai an kammala shari’ar da ake yi.

Daga ƙarshe kotu ta ci gaba da tsaron wanda ake tuhumar har zuwa gama shariiar kuma ba tare da beli ba.

Ana zargin Flower ne da harbe wani mutum, inda aka gurfanar da shi kan zargin kisan a tun watan Agustan 2014.