Wane ne wanda Tinubu ya naɗa a matsayin jagora a Ribas?

Daga BELLO A. BABAJI

Ibok-Ete Ekwe Ibas CFR, tsohon sojan ruwa ne mai muƙamin Mataimakin Admiral, wanda kuma shi ne Shugaban Sojojin ruwa na Nijeriya (CNS) na 22 da ya riƙe muƙamin daga shekarar 2015 zuwa 2021.

Sannan, an haife shi a ranar 27 ga watan Satumbar shekara 1960, kuma ɗan Jihar Kuros-Riba, wato Kudu maso Kudancin Nijeriya.

Ya yi karatun firamare daga 1966 zuwa 1971 a makarantar Nko primary school da Big Qua Primary School a Kalaba, babban birnin jihar.

Daga nan ya shiga Waddell Training Institute, Calabar, daga shekarar 1972 zuwa 1976. A tsakanin 1977 da 1979 ya halarci makarantar School of Basic Studies, Ogoja, kana daga bisani ya shiga makarantar koyon aikin soja ta NDA a 1979.

Ibas ya kuma yi kwasa-kwasan soja da dama a gida Nijeriya da ƙasashen waje, waɗanda daga ciki akwai na Kwalejin Jami’an Sojoji ta Jaji a Kaduna a shekarar 1990.

A watan Yulin 1992 ne Ibas ya halarci tsangayar Amphibious Warfare School ta Jami’ar United States Marine Corps in Quantico dake Virginia a Amurka, inda ya kammala difuloma a watan Mayu, 1993.

Har’ilayau, Ibas ya riƙe muƙamai daban-daban a Rundunar Sojoji ruwa ta Nijeriya, waɗanda akwai zama daraktan jami’an Kwalejin Sojoji ta Jaji daga 2000 zuwa 2002, da wasu manyan muƙamai sakamakon ƙwarewar da ya samu a matsayinsa na babban jami’i.