Wang Yang ya buƙaci majalisar CPPCC ta bada gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma

Daga CMG HAUSA

Shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta ƙasar Sin ta CPPCC Wang Yang, a yau Alhamis ya buƙaci majalisar da ta yi ƙoƙarin cimma muradun al’umma na samun ingantacciyar rayuwa, kana ya bayar da gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma.

Wang Yang ya yi wannan tsokaci ne a wajen rufe taro na biyar na majalisasr CPPCC karo na 13.

Ya ce ya kamata majalisar CPPCC ta sauke dukkan nauyin al’umma dake bisa wuyanta, inda ya buƙaci majalisar da ta saurari muryoyin al’umma domin share musu hawaye.

Ya ƙara da cewa, ya kamata majalisar ta bayar da shawarwari game da hanyoyin da za a cimma muradun al’umma domin kyautata rayuwarsu da kuma taimakawa jam’iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin ƙasar wajen kyautata zaman rayuwar al’ummar ƙasa.

Wang Yang ya kuma yi kira da a aiwatar da matakan kyautata tuntuɓa da kauce wa bin dogayen sharuɗɗa.

Fasaarawa: Ahmad Fagam