Wang Yang ya gana da manyan ƙusoshin majalisun dokokin Mozambique da Burundi

Daga CMG HAUSA

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar Sin (CPPCC), Mr. Wang Yang ya gana da shugabar majalisar dokokin ƙasar Mozambique Esperanca Bias, da ma shugaban majalisar dattawan ƙasar Burundi Emmanuel Sinzohagera, a jiya Talata ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing.

A yayin zantawarsa da Esperanca Bias, Wang Yang ya ce, ƙasar Sin na fatan ƙarfafa aminci, da tuntuɓar juna ta fannin siyasa da manyan tsare tsare tare da Mozambique, kuma ƙasashen biyu su fadada haɗin gwiwarsu, tare da aiwatar da shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, kana majalisar CPPCC na fatan inganta mu’amala tare da majalisar dokokin ƙasar Mozambique, don inganta tushen bunƙasuwar hulɗar kasashen biyu.

A nata ɓangaren kuwa, Madam Esperanca Bias ta bayyana godiya, kan goyon baya da taimakon da ƙasar Sin ke samar wa Mozambique a kullum, kuma ta yi fatan ganin ƙarin nasarori a haɗin gwiwar ƙasashen biyu.

A yayin zantawarsa da Emmanuel Sinzohagera kuma, Wang Yang ya ce, ƙasar Sin na fatan haɗa kai da ƙasashen Afirka, ciki har da Burundi, don tabbatar da shawarar raya duniya, da ma shawarar kiyaye tsaron duniya, a ƙoƙarin kiyaye moriyar ƙasashen Sin da Afirka, da ta ƙasashe masu tasowa.

Kazalika majalisar CPPCC za ta ƙarfafa mu’amala tare da majalisar dattawan Burundi, don ciyar da hulɗar ƙasashen biyu gaba.

Daga nasa ɓangaren, Emmanuel Sinzohagera ya ce, Burundi na dora muhimmanci sosai a kan bunƙasa hulɗarta da ƙasar Sin, kuma majalisar dattawan ƙasar na fatan ƙarfafa mu’amala, da haɗin gwiwa tare da majalisar CPPCC, don kara bunƙasa hulɗar ƙasashen biyu gaba.

Mai fassara: Lubabatu Lei