Daga CRI HAUSA
Babban dan majalissar gudanarwar ƙasar Sin, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya ce Sin na martaba haɗin gwiwar ta da kasashen Afirka, kuma ba ta taba saba alƙawarin ta ba.
Wang Yi, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce cikin shekarun baya bayan nan, Sin ta gina layukan dogo da suka kai tsayin sama da kilomita 10000, da manyan hanyoyin mota masu tsayin kimanin kilomita 100000, da tashoshin ruwa kimanin 100, da kuma tarin asibitoci da makarantu a nahiyar Afirka.
Wang ya ƙara da cewa, ba wani batu na tarkon bashi, sai dai kawai tsabar ayyukan haɗin gwiwa tsakanin sassan biyu.
Ya ce Sin za ta cika alƙawarin ta, na samar wa Afirka alluran rigakafin cutar COVID-19 har biliyan 1, za ta kuma taimakawa nahiyar wajen samar da ƙarin rigakafin a cikin gida, tare da tallafawa nahiyar wajen cimma nasarar yiwa al’ummun ta da za su kai kaso 60 bisa dari rigakafin cutar a wannan shekara ta bana.
Fassarawa: Saminu daga CRI Hausa