Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda huɗu kan warware rikicin Ukraine

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya bayyana matsayin ƙasar Sin da shawarar da ta dauka kan warware rikicin ƙasar Ukraine a halin yanzu, yayin taron manema labarai na taruka biyu da ake gudanarwa Litinin din nan.

Wang Yi ya ce, ƙasar Sin ta yi imanin cewa, idan har ana son warware rikicin da ake fama da shi a halin yanzu, wajibi ne mu mutunta manufofi da ƙa’idojin kundin tsarin mulkin MDD, da mutunta juna da kare ‘yancin kai da yankunan dukkan ƙasashen duniya, haka kuma dole ne mu martaba ƙa’idar rashin raba kan harkokin tsaro, da daidaita matsalolin tsaro na ɓangarori, wajibi ne a martaba sasanta rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da sasantawa cikin lumana, dole ne mu mai da hankali kan ɗorewar zaman lafiyar yanki da samar da daidaito, inganci da dorewar tsarin tsaro a Turai.

Wang Yi ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta yi imanin cewa, yayin da ake ƙara tsananta halin da ake ciki, za a ƙara ci gaba da yin tattaunawar zaman lafiya, yayin da ake ƙara samun sabanin ra’ayi, ya zama wajibi a zauna a yi shawarwari. Ƙasar Sin tana son ci gaba da taka rawa mai ma’ana, wajen shawo kan zaman lafiya, da sa ƙaimi ga yin shawarwari, kuma tana son yin haɗin gwiwa da ragowar ƙasashen duniya, wajen shiga tsakani a lokacin da ake buƙata.

Fassarawa: Ibrahim Yaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *