Wang Yi ya halarci muhawarar babban taron MƊD karo na 77

Daga CMG HAUSA

Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya halarci muhawarar babban taron MƊD karo na 77 a hedkwatar majalisar dake birnin New York na ƙasar Amurka, tare da gabatar da jawabi mai taken “Yin ƙoƙarin don samun ci gaba cikin lumana da kuma ɗaukar alhaki don samun ci gaba ta hanyar haɗin gwiwa”.

Wang Yi ya bayyana cewa, wannan zamani na cike da ƙalubale da kyakkyawan fata.

Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar bisa buƙatun zamanin da ake ciki.

Ya ce ya kamata a kiyaye zaman lafiya, da magance yake-yake. Kana Sin tana son daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.

Ya ƙara da cewa, ya kamata a samu ci gaba a fannin yaki da talauci.

Yana mai cewa, Sin tana ɗaukar aikin samun ci gaba a matsayin muhimmin aiki na ajandar tattaunawa ta ƙasa da ƙasa, don neman samun daidaito daga ƙasa da ƙasa, ta yadda nasarorin da aka samu za su amfanawa kowace ƙasa da jama’arta.

Wang Yi ya ci gaba da cewa, ya kamata a buɗe ƙofa ga ƙasashen waje.

A yi shawarwari don magance tada rikice-rikice, da kin amincewa da tafiyar da harkokin siyasa a cikin ƙungiyoyi da kuma nuna ƙiyayya da juna a cikin ƙungiyoyi daban daban.

Bugu da ƙari, ya kamata a yi haɗin gwiwa da juna, a yi watsi da kiyayya.

Ya ce bai kamata a bambanta ra’ayoyi domin bambancin tsarin ƙasa ba, yana mai cewa, kamata a yi haɗin gwiwa da juna don sa ƙaimi ga samun zaman lafiya da ci gaba tare.

A ƙarshe, ya ce kamata ya yi a tabbatar da adalci ga juna.

A aiwatar da ra’ayin ɓangarori daban daban, da sa ƙaimi ga ƙasa da ƙasa su samu adalci a fannonin kare haƙƙi, da ƙa’idoji, da samun dama, da kuma kafa sabuwar dangantaka tsakanin ƙasa da ƙasa bisa girmamawa juna da adalci da haɗin gwiwa da kuma samun moriyar juna.

Mai fassara: Zainab