Wang Yi ya jajenta wa Ministan Harkokin Wajen Pakistan game da afkuwar ambaliyar ruwa a ƙasar

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya aike da sakon jaje ga takwaransa na ƙasar Pakistan Bilawal Bhutto, kan ambaliyar ruwa da ta afku a ƙasarsa.

Wang Yi ya bayyana cewa, ya kaɗu matuƙa da samun labarin cewa, wurare da dama a Pakistan sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi.

Ya ce, yana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma jajantawa waɗanda suka jikkata, da mutanen yankin da lamarin ya shafa. Ya kara da cewa, gwamnati da jama’ar kasar Sin, za su ci gaba da kasancewa tare da gwamnati da jama’ar Pakistan.

Kuma ya yi imanin cewa, ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Pakistan, al’ummar ƙasar za su iya shawo kan bala’in.

Mai fassara: Bilkisu Xin