Wani mashayi ya daɓa wa jami’in NDLEA wuƙa a Kano

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun cafke wani ɗan shekara 25 mai suna Musa Usman bisa laifin farmakar ɗaya daga cikin su.

Matashin ya daɓa wa jami’in wuƙa ne a yankin Shataletalen Rahama dake ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano.

An kama Usman ne tare da wani abokin aikinsa mai suna Buhari Ya’u Bashir ɗan shekara 24 da wasu kayan maye masu tarin yawa.

Kakakin rundunar na reshen jihar, Muhammad Maigatari ya ce an kama matasan ne a lokacin da suka yi yunƙurin tserewa.

Hukumar ta jaddada aniyarta na cigaba da yaƙi da fatauci ko shan miyagun ƙwayoyi da abubuwa masu sa maye a jihar.

Kakakin ya kuma ce hukumar ta yi alla-wadai da farmakin da aka kai wa jami’in nata, ya na mai cewa za su cigaba da yaƙar sha da fataucin kayan maye.

Wasu daga cikin abubuwan da jami’an suka kama sun haɗa da kilogram 1.1 na tabar cannabis sativa da ƙwayoyin diazepam guda 38 masu nauyin gram 8 da kuma ƙwayoyi 16 na Exol masu nauyin gram 59.

Kazalika, jami’in yaɗa labaran ya ce a halin yanzu mutane biyun da aka kama suna hannun hukumar inda ake cigaba da gudanar da bincike akan su game da laifukan da aka kama su a kai.