
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Asabar ne ƴan sanda a Nahiyar Asiya suka sanar da cewa ce, an kama wani ɗan Pakistan bisa zargin sa da laifin kisa ta hanyar harbe wani admin ɗin dandalin Whatsapp.
An harbe Mushtaq Ahmed ne a maryacen ranar Alhamis a garin Peshawar na birnin Khyber Pakhtunkwa dake kan iyaka da ƙasar Afghanistan, wanda ke da tarihi na zubar da jini a tsakanin al’umma.
Ana dai tuhumar wani mai suna Ashfaq ne da kisan mamacin, kamar yadda rahoton ƴan sandan ya nuna.
Wani ɗan’uwa ga Mushtaq ya ce, an kashe mamacin ne biyo bayan jayayya da aka yi a guruf ɗin, wanda hakan ya sanya Mushtaq a matsayinsa na admin ya cire Ashfaq.
Da farko dai, an gano cewa sun shirya haɗuwa domin yin sulhu a tsakanin su, inda daga baya Ashfaq ya ciro bindiga ya buɗe wa Mushtaq wuta sakamakon fusata da ya yi na cire shi a guruf ɗin da aka yi.
Ana ganin musabbabin faruwar hakan ba ya rasa nasaba da yawaitar makamai a hannun fararen hula da tasirin ƙabilanci da kuma ƙarancin kula da kiyaye dokokin zamantakewa acikin al’umma.