Wani sashe na kotu ya rufto wa Alƙalin-alƙalan Jihar Ekiti

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Alƙalin-alƙalan Jihar Ekiti, Mai shari’a Oyewole Adeyeye, ya tsallake rijiya da baya a ranar Larabar da ta gabata, lokacin da wani sashe na babbar kotun jihar ya rufta masa a lokacin da yake ofishinsa.

A yanzu dai mai shari’a Adeyeye yana samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba a jihar.

Jaridar Manhaja ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da yake bakin aiki ranar Laraba. Alƙalin dai yana ofishinsa ne a lokacin rugujewar.

Wataqila lamarin ba zai rasa nasaba da giɓin tsarin da mamakon ruwan sama ya tsananta ba.

Ba a samu asarar rai ba yayin rugujewar, amma rahotanni sun ce babban alƙalin ya samu munanan raunuka yayin da wani sashe na ofishin ya rufta a kansa.

An ɗauki ƙwaƙƙwaran ƙoƙari daga ma’aikata kafin a ceto alƙali daga baraguzan ginin.

Ziyarar da aka kai ofishin magatakardar don samun ƙarin bayani bai haifar da sakamako ba saboda magatakardar ta hannun wani ma’aikaci ya nemi ‘yan jarida su dawo daga baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *