Wani sirri da ya kamata mata su sani game da kwalliya

Daga QURRATUL-AYN SALIS 

Mata da dama na son sanin sirrin da ke sanya kowacce kyau. A gaskiya zamani ya kaimu lokacin da babu mace mummuna sai dai in ta ga damar zama mummuna. Akwai sirrin kwalliya da dama, ta yadda duk munin mace idan har tana kulawa da su, zai yi wuya a ga muninta. Shi ya sa wasu mazan ke bai wa junansu shawarar gane kyakyawar mace, domin ka da a zo a yi zaɓen tumun dare. Idan mace ta zama mummuna ita ta so. Akwai ababe da dama da ake gyarawa daga yanayin shafa hoda da jan-baki da ja-gira da sauransu.

•Sirri na farko shi ne; mace ta san irin girar da ya kamata ta ja a fuskarta. Misali, idan ke mai fadin fuska ce ja-girarki bai kamata ta yi kama da na mai doguwar fuska ba. Ja-girar mai doguwar fuska ba ta da faɗi. Amma na mai faɗin fuska za a samu da faɗi.

•Kwalliyar mace mai faɗin baki kuma daban take da mace mai tsukakken baki. Mai tsukakken baki ko me ta shafa ana ganin kyawun shi, ba kamar mai faɗin bakin ba. Yana da kyau idan ke mai faɗin baki ce ki samu gazal ɗin baki, ki ja layi a bakin kafin ki shafa walau jan baki ko man baƙi. Yin hakan na rage faɗin bakin.

•Mace mai manyan idanu da wadda ke da ƙananan idanu tabbas kwalliyarsu za ta zama daban. Mai manyan idanu ko ba ta shafa komai ba za ta ganu, kuma ta yi kyau. Amma mai ƙananan idanu sai ta shafa hodar kan ido (eye shadow) domin fito mata da hasken idanunta.

•Kyawun mace mai hanci daban take da mai gajeren hanci. Albishirinku mata! Yanzu akwai hodar da ake shafawa domin miƙar da hanci, musamman ma masu gajerun hanci, amma da ɗan tsada. Kuma za a iya samun irin wannan hodar a manyan kantunan da ake sayar da kayan kwalliya.

•Mace mai kumatu daban take da wadda ba ta da shi; mara kumatu za ta iya shafa hodar ‘blush’ domin inganta kumatunta da kuma ƙara mata kyau. Mai kumatun ma za ta iya shafa wannan hodar, amma sai ta ga dama domin in ta bari a hakan ma kyau za ta yi.