WASIƘU: ‘Babu alamar kasafin kuɗin 2022 zai taimaki talaka’

*Ya kamata talaka ya san cewa Allah kaɗai ne gatansa
*Shan miyagun ƙwayoyi: Babbar barazanar da ke neman kassara matasan Nijeriya

Assalamu alaikum, jarudar Blueprint Manhaja. Haƙiƙa mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da su ke yi mana ƙaiƙayi a rai tare da isar da saƙon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar ƙasa. Muna muku addu’ar Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasar wannan jarida mai farin jini baki ɗaya.

Abin kunya ne kwarai da gaske a irin halin da wannan ƙasa tamu da ma al’umma musamman ma’aikata ke rayuwa cikin ƙunci a ce shugaba Buhari ya ware wasu kuɗaɗe domin amfanin kansa da kansa, wanda kuɗin abincinsa kaɗai na rana guda ya kai albashin sama da mutum biyar.

Inda idan aka kasafta kuɗin abincinsa na rana ɗaya izuwa gida biyar, za su kama naira dubu hamsin da uku da ɗari takwas da sittin da uku (N53,863). Wanda wannan abin kunya ne kwarai da gaske a ƙasar da Naira 30,000 ke neman gagara a matsayin mafi ƙarancin albashi, a kuma ƙasar da albashin ma da ƙyar ake iya biya.

Sannan a ce an ware sama da miliyan arba’in domin sayen ruwa da lemu, wanda kuɗinnan baki ɗaya za su zarare ne a tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Babu shakka wannan kasafin kuɗi ba a yi domin talaka ya amfana ba, sannan duniya za ta kalli shugaban da ake cewa mai adalci a matsayin marar tausayi idan aka yi duba da irin halin ƙunci da talauci da talaka ke fuskanta a halin su kuma a ƙarƙashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Lokaci ya yi da ’yan Nijeriya za su fahimci cewa, shugaba Muhammadu Buhari ba fa talakawa ba ne a gabansa. Domin ya bi duk inda talaka zai amfana da shi ya rage kuɗin, sannan ya qara wa wurare marasa amfani kuɗaɗe masu yawan gaske. Gaskiya mu dai talakawa sai dai mu koma ga Allah, sannan mu ci gaba da addu’a a kan Allah ya kawo mana sauƙin rayuwa.
Wassalam.

Daga Ahmad Musa, 07041094323.

Ya kamata talaka ya san cewa Allah kaɗai ne gatansa

Assalamu alaikum, Jaridar Blueprint Manhaja. A zahirance, rayuwa tana kyau ne da abubuwa uku. Lafiya, abinci da mazauni. Waɗannan sinadaran da suke inganta rayuwa sun zama watan sallah a wurin talaka. Ba kowa ne yake gani ba.

Lafiya ba ta ishe shi ba, bai da gida, bai da abinci, bai da matsuguni. Wurin kwanan sa shi ne inda ya samu wurin kwanciya ko a ina ne. Idan ana rana a kwanyar kansa zafin zai kare a kansa. Idan ana ruwa tamkar kifi haka zai zama. Irin waɗannan mutane suna da haƙƙi a wurinmu. Suna da haƙƙi a wurin gwamnati. Ba zaɓin su ba ne su kasance haka, amma zaɓin gwamnati ne ta bar su a haka. Haka kuma zaɓin mu ne mu bar su a haka. Gwamnati tana da wadataccen arziki da za ta iya shiri na musamman ga irin waɗannan bayin Allah. Amma ko kaɗan hukumomi ba su du ba saboda ta wannan ɓangare hatta masu gidan ma ba su tsira ba. A iya sani na, kusan kowani ɓangare a Nijeriya na fama da ambaliyar ruwa a cikin wannan.

Daga Husain Musa, 09037353330.

Kisan Hanifa a Kano

Ga dukkan alamu nesa ta matso kusa ta fuskar aikata ta’addanci, maganar ta bi shanun sarki ta ɓata. Da farko ina ƙara miƙa ta’aziyya da addu’a ta jaje ga mahaifan Hanifa wato, Malam Abubakar da Murja. Allah ya jiƙanta ku kuma da sauran dangi duka ya ba da haƙuri da juriya. Na tabbatas waɗanda duk su ka tabbata da hannu a wancen mugun aiki za su girbi abinda su ka shuka ta fuskar hukumci.

Ba kisan Hanifa kaɗai ne aka aiwatar ba domin a 2021 a Jihar Kaduna a Unguwar Badarawa an sace tare da kisan wani yaro. Kuda abinda duk ke ƙara ta’azzara waɗancan munanan laifuka rashin yanke hukunci da aiwatarwa ne. Abin takaicin irin waɗancan masu laifuka na kisa su na nan a gidajen kaso aje ba hukunci, wanda idan da duk wanda yayi za a yi masa da tuni an samu sauƙi na kisa da zubar da jinanen al’umma a arha. Mu na fatan kar kisan marigayiya Hanifa ya zamo an ja jiki wajen yanke hukumci na gaskiya da gaske ga makashin ta, domin hakan ne adalci.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519, 08080140820.

Shan miyagun ƙwayoyi: Babbar barazanar da ke neman kassara matasan Nijeriya

A wannan makon, wasiƙata za ta duba batun annobar ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi a tsakanin rukunan al’ummar Nijeriya ne musamman matasa, domin wata babbar barazana ce da tarnaƙi a ci gaban zamantakewa, tsaro da tattalin arziki.

Matsala ce mai wuyar magani wadda a kevance ɗaya ce daga cikin gagararrun matsalolin da suka gunduri kowa, waɗanda suka tsunduma sabbin jinin shiga mawuyacin hali da yawaitar ayyukan ashsha.

Masana sun tabbatar da cewa al’adar amfani da miyagun ƙwayoyin ba a kan daidai ba, ya na da alaƙar ƙut-da-ƙut wajen yaɗuwar miyagun laifuka a ƙasar nan. Bil hasali, yanayin da ya jawo garƙame matasa da dama gidajen kaso, a cikin lungu da saqo, a faɗin ƙasar nan. Wanda ko shakka babu, shan miyagun ƙwayoyi tare da dangogin sa ya tsunduma matasan a cikin halin ni’asu.

Sannan duk da matakin da gwamnatoci ke ɗauka wajen yaƙar wannan annoba, ta hanyar kafa hukumomin yaƙi da sha tare da fataucin ƙwayoyin, kamar hukumar NDLEA da aka kafa a 1999, da masu alaka da ita, waɗanda ke kai gwauro-mari wajen daqile yaɗuwar lamarin sha tare da safarar ƙwayoyi masu sa maye a ƙasar nan, amma lamarin ya ci tura, ganin har yanzu an kasa kaiwa ga manufar da aka samar dasu.

A halin da ake ciki yanzu, duniya ta na fuskantar babban ƙalubalen mummunan sauyin da waɗannan gagararrun matsaloli, waɗanda ke neman canja alƙiblar matafiyar al’ummar duniyar: shan miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, fama da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan adam (HIV/AIDS), haɗi da gurɓatar yanayi.

Wanda shan kwayoyi ba bisa ƙa’ida ba da safarar su ke nema ya gagari kundila, sannan kuma barazanar da ke neman karya ƙashin bayan ci gaban matasa a kowacce ƙasa. Matsala ce babba, wadda har yanzu ba a gano lagon ta ba, musamman yadda abin ya fi kamari ga matasa masu jini a jika; ɓangare muhimmi a ci gaba tare da kiyaye diyaucin kowacce ƙasa a duniya.

Kuma kamar yadda masana suka bayyana, shan miyagun ƙwayoyin wata mummunar al’ada ce wadda ta zama ruwan dare a tsakanin kowanne ɓangare na al’umma – maza da mata, yara da manya. Sannan ta’asa ce wadda ta shafi kowanne mataki na al’umma da mu’amalar yau da kullum. Lamarin da ya kaiwa kowa a wuya- saboda bayyanar sa a sarari tare da ɗanɗanar kuɗar sakamakonsa ga al’umma.

A wani bincike wanda cibiyar nazarin amfani da magunguna ba a bisa ƙa’ida ba, kana da gano illolin da hakan ke haifar wa, ta ankarar da cewa tun a tashin farko ana iya gano yadda shan miyagun ƙwayoyi zai yi illa ga rayuwar mutum – a rayuwar matasa, idan sun girma: musamman ga matasan da suka fara ta’ammuli da qwayoyi a shekaru 14 – tasirin miyagun ƙwayoyin zai bayyana ne daga shekarun su na 21 zuwa abinda ya yi sama.

Daga Mustapha Musa Muhammad, Ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *