WASIƘU: Illar cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a (1)

*Cire Nijeriya daga cikin masu tauye ’yancin addini

Assalamu alaikum, da fatan kowa muna lafiya, ameen. Mu sani cewa, kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsa mummuna ko kyakkyawa, wasu kam ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai.

Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce kowa ya tsaya a kan nasa, kada wani ya ce dole sai kowa ya bar nasa ya dawo nasa. Idan kowa ya riƙe nasa, to ba yadda za a a ce an samu wata hatsaniya game da fahimtar wani. Kamar yadda karin maganar Hausawa ke cewa ‘DUNIYA ZAMAN ƊAN MARINA, KOWA DA INDA YA SA GABANSA!’

A irin wannan yanayi ne ya zama sai ka taras da wani ko wasu suna furta kalaman da za su kawo ruɗani da wani, wani lokaci ma har yakan kai ga jawo tashin hankali a tsakanin jama’a. Duk irin waɗannan abubuwa, ba wani abu ke jawo su ba illa rashin girmama addini, fahimta, ƙabila ko martabar wani, wanda hakan kuma ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar al’umma. Domin wajibi ne, muddun ana tare, to a girmama juna.

Kalaman cusa kiyayya, ko kalaman ɓatanci, dukkansu abu ɗaya ne, domin ba abin da suke jawowa illa rarraba da tashin hankali a tsakanin jama’a. Wasu lokuta ma, abin takaici za ka taras da irin waɗannan kalaman suna fitowa ne daga bakin shugabannin addini, waɗanda suka haɗa da Malamai da Fastoci, wanda maimakon su zama masu haɗa kan al’umma, sai ya zama sun zama masu rabawa, ta yadda za ka ga wasu shugabannin addinin sun bar koyarwar addinin nasu sun koma suna bin ra’ayin kansu, kuma da haka suke jan magoya bayana.

Haka kuma ko ma a cikin addinin, mutum zai taras da cewa ya-su-ya-su ma suna cusa irin wannan kiyayya ta hanyar furta kalaman ɓantanci da cusa kiyayya ga mabiyansu na sauran al’ummar da suke da bambancin fahimta kom ra’ayi da su, inda a wasu lokuta abin har ya kan kai ga zubar da jini. Abin bakin cikin ma wasu lokuta za ka taras da ’yan gida ɗaya ne, amma ba a ga-maciji da juna.

Baya ga addini, wani ɓangare kuma da ake amfani da irin waɗannan kalamai na cusa kiyayya a tsakanin al’umma, shi ne ɓangaren siyasa, wanda za a iya cewa kamar abin ya fi muni ta nan. Domin za ka ga ɗan siyasa ya dage yana ta furta kalamai na vatanci, wanda zai cusa mummanar ƙiyayya idan abokin hamayyarsa ya ji, wanda ta haka sai ya a ginu a cikin ƙiyayya da gaba.

Baya ga fannonin addini da siyasa, hatta a tsakanin jama’a ma akwai lokutan da wasu jama’a za su riƙa furta irin waɗannan kalamai na cusa ƙiyayya da ɓatanci, wasu lokuta kawai don su haddasa gaba da ƙiyayya, ko kuma don cimma wata manufa tasu ta kashin kansu. Ta yadda za ka ga wasu lokuta ko a cikin hira ma sai kawai ka ji mutum ya soka wa ɗan uwansa wata magana, wanda in ba hankali aka yi ba, nan da nan sai a tashi da tsiya.

Duk idan muka bi waɗannan fannoni na addini, siyasa da zamantakewa, za mu ga cewa babu buƙatar a rinƙa tofa, ko furta irin waɗannan kalamai. Domin a har kullum babu wani abu da suke haifarwa, kamar yadda na faɗa a sama, illa gaba da ƙiyayya, wasu lokuta ma har ta kai ga zubar da jini, wanda idan da an bi abin da ya dace, to hakan ba za ta faru ba.

Ana samun saɓanin ra’ayi tsakanin KALAMAN CUSA ƘIYAYYA da kuma HAƘƘIN FURTA ALBARKACIN BAKI. Waɗannan abubuwa guda biyu suna da bambanci sosai a tsakaninsu. FURTA ALBARKACIN BAKI, wata dama ce da mutum ke da ita na faɗin ra’ayinsa game da wani, ko wasu ko shugabanninsa, waɗanda yake ganin idan faɗa ƙila a gyara, ko kuma ya fahimtar da wasu game da abin da yake faɗi. Amma ba zai zama ya yi amfani da wannan dama don zagi ko jawo gaba da ƙiyayya ba.

Sannan KALAMAN CUSA ƘIYAYYA, waɗannan a bayyane suke, wato kalamai ne da mutane kan yi don kawai su jawo ƙiyayya da tsana a tsakanin jama’a. Da irin wannan wasu ke ganin cewa wai idan an hana su furta wasu kalamai, ko an kama su don sun yi haka, sai su rinƙa ganin tamkar an tauye masu haƙƙi ne faɗin albarkacin baki, musamman a tsarin mulki irin na dimokraɗiyya.

Za mu kwana a nan. A makon gobe in Allah ya yarda zan ci gaba da bayani a wannnan a shafi mai albarka ta wasiƙu game da yadda gwamnatin ta ɗauki wannan abu, sannan da yadda wasu masana a harkar Shari’a suke kallon abin.
Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun injiniyan Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Cire Nijeriya daga cikin masu tauye ’yancin addini

A makon jiya ne kwana guda kafin ziyarar Antony Biliken a Nijeriya, ƙasar Amurka ta cire sunan ƙasarmu a cikin ƙasashe da ta ke kallo ko tuhuma da tauye ’yancin gudanar da addini. Mu tun kafin a ayyana hakan samsam ba mu amince da cewa an hana gudanar da addini ba. Amma mu na sane da cewa a dokar ƙasa duk wani ko wasu da ke gurin tayar da husuma ko neman a ware wanda ka iya janyo fitintinu wannan ne gwamnati ke hanawa tare da ɗaukar matakin dalilewa. Ko shakka babu waɗanda ke suka da kuma ihu cewa a na take ’yancin addini wannan ruwan su kuma hujja ce mai iya tabbatarwa ko kuma rashin hujja ya ƙaryata zargin.

Ina jawo hankulan duk waɗanda su ka amince da cewa laɓewa da addini a tada husuma mu a musulumci babu wanda duk ya yi hakan ra’ayinsa ne. Ita kuma gwamnati ta ƙara kula kama mai laifi da hukumci na daidai laifi ta hakanne za a rage matsaloli na yawaitar muggan laifuka a cikin al’umma musamman manyan laifukka.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa, 07066434519/ 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *