WASIƘU: Ina mafita ga almajiranci?

Assalamu alaikum. A yau zan aika buɗaɗɗiyar wasiƙa ne na ina mafita ga Almajiranci a Nijeriya. Almajiranci na da ma’ana guda biyu, wato tsarin koyar da ilimin addinin musulunci a ƙasashen yammacin Afirka, musamman a arewacin Nijeriya, yadda ake tura yara wajen Malamai a wasu garuruwa domin yin karatun Ƙur’ani. Ɗaya ma’anar ita ce ta tsarin da irin waɗannan ɗalibai da kuma waɗanda ba ɗaliban ba ke yawo su na barar abinci ko kuɗi. Almajirancin da mu ke gani a yanzu ya sha banban da wanda aka gada a can baya.

A baya almajiranci shine rumbun da ake samar da Malamai, limamai da masu wa’azi, domin a doron wannan tsari ne Usman Ɗanfodio ya taso har ya yi jihadin da ya samar da daular Usmaniyya wadda ta ture mulkin zalunci na habe ta kafa daular musulunci mai adalci, zaman lafiya da ilimi a yawancin sassa na arewacin afirka kusan sama da shekaru ɗari.

Wayewar rubutu da karatu na ajami ya samar wa daular damar kafa tsari na mulki a faɗin daular cikin sauƙi. Makarantun allo su ne su ka zama wasu jami’o’i da ke samar da ƙwararrun Malamai da ɗalibai cikin tsarin tarbiyya, juriya da girmama na gaba. Zuwan turawa sun kwaikwaiyi tsarin ta hanyar samar da makarantun kwana na boko.

Bayan turawa sun kafa mulkinsu na mallaka, cikin kutungwila, sun kawo canje-canje waɗanda su ne ummul aba’isun karya tsarin makarantun allo. Ragewa sarakunan gargajiya iko, waxanda su ke bawa Malaman allo gonaki waɗanda almajiransu ke nomawa domin samar da abincin da za su ci, sannan su ke tattara sadaka da zakka da ake kaiwa makarantun, ya kawo durƙushewar tsarin ciyarwa a makarantun allo.

Iyaye na kawo amfanin gonar da suka shuka wajen Malaman domin ciyar da yaransu da ke almajiranci. Rushewar wannan tsari ya jawo dole Malamai ke tura yaransu yin bara domin samo abincin da za su ci. Sannan a baya ana tura yara almajiranci bayan sun tasa sosai sun kai shekaru goma zuwa sama. Haƙiƙa zuwan bature na daga cikin abinda ya fara karya tsarin almajiranci.

A yau almajiranci ya rasa irin darajojin da aka san shi da su a baya ya zama wata annoba ga almajiran kansu, malamansu, iyayensu da kuma al’umma. Domin a yanzu ka na iya ganin yaro ɗan shekara 4 an turo shi almajiranci, abinda babu shi a baya. Rashin imani ne idan aka kalla ta kowacce fuska, walau ta fuskar addini, al’ada ko tattalin arziki, tura ɗan ƙaramin yaro mai shekara huɗu zuwa almajiranci ko da Almajirci irin na da ne ba na yanzu ba.

A addinance ko sakin matarka ka yi ba ka da ikon karve yaro da ya gaza shekaru 7 aqalla. Sannan binciken kimiyya ya tabbatar da cewa shi yaro daga haihuwa zuwa aqalla shekaru 10 ya na buƙatar kasancewa kusa da uwarsa domin Allah ya halicci mutum da ɗabi’u waɗanda sannu a hankali su ke bayyana daki-daki a rayuwar yara sakamakon mu’amala da uwa, uba, ’yanuwa da makwabta.

Misali halayyar tausayi ko soyayya ko sanin ya kamata mu’amala da uwa ke saka na yaro su bayyana gare shi kum ya gane ya riqe su a kwakwalwarsa. To a duk sanda aka raba yaro da uwarsa ya na rasa wannan mataki da ke zungurar boyayyun halayensa.

Binciken shahararren masani Sigmund Freud ya tabbatar da cewa akasarin mutane da ke zama mugaye marasa imani a lokacin da su ka girma, idan an binciki shekarun yarintarsu akan tarar sun rasa waccan irin kyaykyawar mu’amala musamman da uwa. Sakamakon haka su kan kasance marasa tausayi kuma ɗabi’ar da ke saka da-na-sani na da rauni cikin halayyarsu.

Abubuwan da ke faruwa yau a arewacin Nijeriya na tabbatar da gaskiyar wannan bincike saboda yawancin ‘yan boko haram da masu satar mutane na da irin wannan halayya ta rashin imani da halin da-na-sani. Domin sun taso babu shakuwar iyaye da al’umma don haka su ke kallon kowa a matsayin makiyi saboda su ma babu wanda ya tausaya musu.

Asarar da tsarin almajiranci ke jawo mana na da yawa: ya na hana yara ilimi, samun soyayyar iyaye, jefa su cikin haɗurra da ke tauye rayuwarsa ko zama annoba ga al’umma. Dole duk masu ruwa da tsaki, musamman hukumomi su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin an kawo canji a tsarin, ta hanyar saka shi cikin tsarin ilimi na ƙasa.
Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, 08168716583

Illar cin hanci da cin dunduniya

Assalamu alaikum! Yawancinmu ’yan Nijeriya mu kan kasance Jahilan masu ilimi ne, wato za ka ga cewa duk da cewa mun yi mu’amala iri-iri ta rayuwa kuma mun je makaranta mun sami difloma, digiri ko digirgir, tunanin mu yakan kasance a gajeriyar mahanga yadda komai mu ke kallonsa daga ɓangaren yanki, addini ko ƙabila, kamar yadda malamai ke yawan cewa, shi jahilci ba wai kawai yana nufin rashin iya karatu ko rubutu ba ne, fyace ana aiki da shi yadda ya kamata.

Mu yi ƙoƙarin ganin ba mu zama misalin Jaki da kaya ba. Mun kasa gane cewa manyan ƙasarnan sun kasance a mu’amalar rayuwarsu da ta ’ya’yansu babu ruwansu da addini, ƙabila ko yanki, su kan haxa kai wajen ganin sun sace arzikin ƙasa da barin talakawa cikin wahala. Duk matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a yanzu idan ka bi asalai za ka iya alaƙanta sanadiyar daga cin hanci da rashawa.

’Yan Nijeriya mu farka daga barci, mu tashi tsaye wajen yi wa kan mu adalci. Mu riƙa kallon ƙasarmu ta mahangar gaskiya, ‘yan uwantaka da tsira tare ba ta mahangar ɓangaranci kowanne iri ba.

Mun fi kowa son addini, musulminmu da kiristanmu, ga yawan faɗar Allah a baki ko yaushe, amma babu Allah cikin zukatanmu. Annabi isa na cewa, “Gaskiya ce kaɗai za ta tserar da mu”, sannan mu ɗin ga yi wa mutane hukunci kawai daga irin aikin da su ka aikata. A Kurani Allah ya umarce mu da mu zama masu adalci da faɗar gaskiya ko a karan kanmu ko iyaye da ‘yanuwa ba banbanci tsakanin attajiri da mawadaci. Mu haɗa hannu mu yaƙi cin hanci da rashawa mu kashe ta da kanmu.

Daga Ahmad Musa, 07066778190.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *