WASIƘU: Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya

*Zaɓen Anambara: Darasi ga Arewa
*Matasa mu kama sana’a

Nijeriya dai wata babbar ƙasa ce a yammacin Afrika, wacce Allah ya albarkace ta da tarin ni’imomi da albarkatu masu yawa. Kama daga yawan jama’a da suka haura miliyan 200, da kuma ma’adinan ƙarƙashin ƙasa, na ruwa da na kan tudu, wanda ba kowacce ƙasa ce Allah ya bai wa wannan arzikin ba. Sai dai kuma ƙalubale iri iri da suka haɗa da rashin shugabanci nagari, cin hanci da rashawa, ƙabilanci da ɓangaranci, da kuma uwa uba matsalar taɓarɓarewar tsaro.

Sai dai duk da ƙoƙarin da masu riƙe da madafun iko, ƙwararru da rundunonin tsaron ƙasa suke cewa suna yi don shawo kan waɗannan matsaloli da suka dabaibaye ƙasar nan, har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba. ’Yan Nijeriya na ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da talauci, harkokin tafiyar da gwamnati sai ƙara lalacewa suke yi saboda rashin kishin ƙasa da ayyukan rashin gaskiya da suka yi yawa, ga kuma ƙaruwar ƙungiyoyin ’yan ta’adda da tsagera da suka yi yawa a cikin qasa, suna haifar da firgici a zukatan ’yan Nijeriya da asarar rayuka da dukiyoyi.

Lallai akwai buƙatar hukumomi su tashi tsaye su ga sun samar da sauyin dabaru da tsari a irin matakan da suke ɗauka, saboda rayuwa kullum ƙara sauyawa take yi, kuma su ma ɓata gari canza salo da dabaru suke yi.

Daga cikin matakan da ya kamata a bi wajen magance matsalolin tsaro a Nijeriya sun haɗa da daƙile cin hanci da rashawa. Domin kuwa cin hanci da rashawa babbar hanya ce ta maganin matsalolin Nijeriya, tun daga kan shugabanni har zuwa ga talakawa.

Sannan wajibi ne a ƙarfafa tare da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri, saboda gano irin maƙarƙashiyar da wasu ɓata gari daga ciki da wajen ƙasar nan suke ƙoƙarin haddasawa ta hanyar amfani da wasu baragurbin ’yan ƙasa suna haifar da yamutsi nan da can, domin karkatar da tunanin hukumomi da jami’an tsaro wajen kunna wutar futintinun da ba za a gano tushen su da wuri ba, ballantana a samar da mafita. Matuƙar aka yi qoqari aka toshe wannan hanya to, lallai akwai kyakkyawan zaton za a samu sauƙin taɓarɓarewar gsaro a ƙasar nan.

Haka kuma har wa yau daga vangaren yadda jami’an tsaro ke amfani da ’yan jarida da kafofin sadarwa na zamani wajen yaɗa farfaganda da kururuta ayyukan da suke gudanarwa, don jawo ra’ayin jama’ar ƙasa. Hakan yana da muhimmanci, amma kuma yana da haɗari. Magance matsalolin tsaro tana da buƙatar sirri ne sosai da Kuma ƙwararrun ma’aikatan tsaro da sabbin dabaru. Abin nufi a nan shi ne, dukkan wani aiki da aka shirya za a gabatar da shi bai kamata a yi ta yaɗawa a kafafen sada zumunta ba, saboda fitar da wannan sirri zai sanya waɗanda za a kai wa samame ko farmaki, su su sake sabon shiri. Amma matuƙar aka bar Al’amarin a cikin Sirri haƙiƙa suna masu sakankancewa za a ci galaba a kansu. Babu shakka wannan ma hanya ce mai ɓullewa wajen magance matsalar tsaro.

Bisa la’akari da yawan jama’a da Allah ya albarkaci ƙasar nan da shi, ya zama tilas ga hukumomi su magance wannan matsala, wajen samar da guraben ayyukan yi, domin ɗauke tunanin matasa daga shiga ayyukan da ba su kamata ba. Yana da kyau wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro a tantance waɗanda suke da kishin ƙasa kuma ba a san su da mummunan halayya ba, ba wai kawai a dinga ɗiban yara ƙara zube ko waɗanda ke da gata da ɗaurin gindin manyan ƙasa ba, waɗanda babu abin da za su iya yi wa kansu sai sharholiya, da ƙara ɓata ƙasa.

Daga ƙarshe muna fatan Allah ya tabbatar mana da tsaro a ƙasarmu Nijeriya, ya kuma bamu lafiya da zaman lafiya baki ɗaya.

Daga Mannubiyya Abdulƙadir Mu’azu, wata marubuciya da ke zaune a Jos, Jihar Filato, [email protected]

Zaɓen Anambara: Darasi ga Arewa

Ina ma a ce jama’ar arewa za mu nutsu mu ɗau darussa daga duk wasu zaɓe da a ke gudanarwa a yankunan kudanci wanda bambancin jam’iyya bai ma su tasiri na ƙin juna da ƙulla gaba ba. A jihar kano bayan zaɓen 2019 hukumar zave INEC ta sanar da cewa zaɓen farko bai kammala ba wato ta zamo ‘Inconclusive’ inda a nan ne jama’a da dama kowa da tasa fassarai haka a Jihar Sokoto an kammala wasu rumfunan kamin a saki cikakken sakamakon. Yau a Jihar Anambra zaɓen farko ya zamo ‘Inconclusive’ Jam’iyyu 4 ne su ka fafata wanda a ƙarshe APGA mai mulkin jihai tai nasara da ƙuri’u.103,946. Sai PDP 51,322 da APC 42,942. Ta huɗu YPP 20,917. Amma babu qorafin ɓatanci ga junansu. Sai a ƙarashe wato ‘Inconclusive’ na a Jihar Kano wanda dukkanin mu addini da al’adu da harshen mu duka ɗaya. Lallai a Arewa da saurammu a harkar siyasa ta mutumta juna da juriya, mu ne ya fi cencenta mu ba da misali mai kyau ga wasummu abokan zama.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa katsina, 07066434519/08080140820.

Matasa mu kama sana’a

Assalamu alaikum. Haƙiƙa ba ƙaramin tashin hankali ba ne, a ce an wayi gari matashi ba ya da takamaiman wurin da zai je domin neman na kansa. Rashin  hakan ne ke sa ɗimbin matasa aukawa cikin miyagun ayyuka irin su; sace-sace da shaye-shaye da bangar siyasa da sauransu. A wani ɓangaren ma sana’a ta fi muhimmanci fiye da wani ilimin, dalili shi ne sau tari matasa da yawa masu ilimi sukan yi amfani da iliminsu ta hanyoyin da ba su dace ba, sakamakon rashin sana’a inda wani lokacin ma ba za ka iya bambance matashi mai ilimi da marar ilimi ba, kamar wajen shaye-shaye da sace-sace inda dukansu sukan shiga riga iri ɗaya.

Saboda haka nake kira ga ’yan uwana matasa, masu karatu da marasa karatu cewa, mu fantsama ga harkokin kasuwanci domin neman halal ɗinmu da taimakon kanmu da iyayenmu, maimakon ci gaba da zaman muna jira daga wajen gwamnati ko iyayenmu. Lokaci ya yi da za mu farka daga dogon barcin da muke.

Ta yaya za mu fara kasuwanci?  Wannan tambaya ce mai ma’ana ganin cewa akwai sana’o’i da yawa waɗanda gurvatattu ne. To amma a nan muna magana ce a kan sana’o’i na halal musamman waɗanda muka gada daga wajen iyaye da kakanni. Misali akwai, noma da ɗinki da fatauci  da sauransu. Akwai kuma na zamani waɗanda yanzu su ma za mu kira su da sana’a domin ta nan mutane da yawa suke cin abinci, kamar kasuwancin Intanet da kayan shago da ɗaukar hoto da wankin mota da ginin zamani da kabu-kabu da sauransu.

Kaɗan daga cikin sana’o’in da na lissafo, wasu suna buƙatar jari don farawa, wasu da yawa a cikinsu kuma kawai biyayya da neman izini suke buƙata daga wajen iyayen gida masu yin irin wannan sana’a don farawa a matsayin yaro kafin kai ma ka koya a kai ga lokacin da kai ma za ka buɗe naka wajen sana’ar ko kasuwancin tare da janyo waɗansu yaran don koya musu. Amma fa duk hakan zai faru ne in an yi haƙuri. Allah Ya sa mu dace, Ilahee Ameen.

Daga Mustapha Musa Muhammad, Xalibi a fannin karatun injiniyan Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.