WASIƘU: Matasa a siyasar intanet

*Alƙawarin ɗan siyasa
*Kira ga masu neman takarar shugabancin Nijeriya a 2023

Assalamu alaikum. Wata babbar cutar da ke damun matasanmu ita ce rashin sanin yakamata, da kuma jahilci. An mayar da zauren sada zumunta na intanet wani fagen barkwanci, wani lokacin kuma fagen fama inda ake buɗe wuta da kalamai, musamman matasa masu son wasa iyayien gidajensu a siyasance, ta yadda a yawaita yabo ko zagi kamar zogale.

Wannan annamimancin na faruwa tsakanin ’yan adawa, ‘yan jam’iyya ɗaya ko ma ’yan uwa ‘yan gida ɗaya. Duk da mun san cewa talauci da jahilci suna taka rawar gani a wajen aiwatar da waɗannan ɗabi’un, amma sau da yawa sai ka ga masu waɗannan halayen mutane ne masu ilimi yayin da suka dawo gida sai a hau Facebook ko Whatsapp a riƙa tura makamai ana sauke boma-bomai!
Duk da zage-zagen da banbadancin har yanzu ba wanda aka ba mota ko wasu maƙudan kuɗaɗe ya je ya yi sharholiyarsa a nan gida ko a ƙasashen waje. Wai ta wacce hanya ce ma uban gidanka zai nuna yana godiya ko ba ka kyauta?

Wai shin ma matasa sun shirya karɓar mulki daga ruvavvun dattijan nan kuwa? Ko dai kwambala ce! Yana da wuya a amincewa mutum ɗaya don yana kyautata muku ku kaɗai, duk da kowa yana da ’yancin zaɓar gwaninsa.

Wani abin dubawa shi ne, ’ya’yan waɗannan mutanen suna Turai, wasu ma basu san kuna yi ba, to me zai sa ku riƙa ɓata lokacinku wajen wasa wasu, kun mayar da kanku bayi, ba boko ba Arabi ko ga karatu ba ilimi balle wayewa, kakanninku sun fi ku fahimta.

Lokaci ya yi da matasa zasu gane, su tabbatar da cewar su ke kawo canji, kuma matasa suna da daraja, musmamman lokacin da aka busa ƙahon siyasa. Ku ke zavo shugabannin da suke tatsarku, su tsotse fetur. Ku yaƙi kwaɗayi, da son duniya. Kuɗinku ne, haƙƙoƙin naku ne, ta ya ake juya ku kamar waina?

Tabbas kafin a yi nasara sai an yaƙi son rai, a riƙa fito da ra’ayoyi masu ma’ana, koda baka taɓa cin kwabon wani ba, idan yana kyautatawa tare da nuna halin dattako ga ’yan uwansa na jini, makwafta, abokai, matafiya, sannan ya kasance mai sauƙin kai da akin hannu, mun sami ɗan takara! Kar mu tsani mutum don ba ya bamu albashinsa ko baya muku dariya ko sallama, kowa da halitarsa, kuma kar ku manta abota ba ta dawwama a siyasance! Duk abin da za mu yi, mu yi don Allah.

Kira ga matasa; ina kira ga matasa dole ne ku tashi tsaye, ku cire tsoro da ragwanci, ku fito a fafata da ku a cikin duniyar neman ’yanci da sanin kai. Matasa lokaci yayi da ’yan siyasa za su daina amfani da mu wajen cimma burinsu, da manufofinsu wanda ba cigaban al’umma ba ne, kuma bana kishin ƙasa ba. Matasa lokaci ya yi da za mu nuna wa ’yan siyasa cewa kan mu a haɗe yake, su daina ba mu makamai da kayan maye muna halakar da junanmu saboda cikar burinsu da kuma kariya ga jam’iyyunsu. Matasa mu fito mu gaya wa ‘yan siyasa, mun daina siyasar duhun kai, mun daina siyasar kuɗi ko jam’iyya.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a Fannin Karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Kwalejin Fasaha ta Tarayya ‘Federal Polytechnic’ Kaduna, 09123302968.

Alƙawarin ɗan siyasa

An ce alƙawari kaya ne, zai fi dacewa idan mutum na nema duk wani muƙami ya kyautata niyya kuma ya riƙa bibiyar tarihi na waɗanda su ka gabata a wannan fage a nan zai ɗauki darussa. Duk da cewa ba ai ma mutane duka kuɗin goro ta fuskar nagarta ko akasin ta amma dai a gaski ɗabi’u na ’yan siyasa a wannan lokaci sai sannu wato kamar yadda sauran al’ummai ta ke haka waɗancan ake samun su ta fuskar cika alƙawurra da kwatanta gaskiya da adalci kaɗan ne a cikin sauran jama’a haka kaɗan ne a cikin ’yan siyasa don haka mu gaya ma kawukanmu gaskiya ta fuskar lalubo da gano mafita.

Talakkawa a kullum ba a samun rayuwa tai sauƙi har sai idan mu kammu sauƙin ne a tsakaninmu. Amma jama’a ta zamo mai hassada da kyeta da ƙin son gaskiya kuma har mu ce tilas rayuwa ta yi kyau, anya? Bayan haka, kai ɗan siyasa ina ma ace alƙawurra da ka ɗauka za ka tuna kafin ku wasu ne kar ka yi nadama marar amfani a wannan rayuwai. Wannan shawara ce ba bu tilas.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519, 08080140820.

Kira ga masu neman takarar shugabancin Nijeriya a 2023

Assalamu alaikum, Blueprint Manhaja, ina so ku bani dama na faɗi damuwata akan ‘yan siyasarmu, masu neman takarar kujerar shugabancin Nijeriya a zaɓe mai zuwa na 2023.

Da farko dai ya kamata su sani zamani da yanayi na duniya ya canja an wuce ƙarnin da wasu tsuraru za su ci gaba da kwashe arzikin ƙasarmu suna kaiwa Turai suna azurta kansu da ’ya’yansu. Mu mun sani mafi akasarin waɗanda shugaban ƙasa ke tare da su da sanatoci da gwamnoni ba ƙaunarsa suke ba. Asali ma suke kawo ɓatanci da daƙile duk wani abu da zai kawo ci gaban a ƙasa don sanya wa talaka ƙiyayyar wani a cikin zuciyarsu. Sun manta cewa Allah ne ke bada mulki. Kuma mun yi imani Allah zai ba mu wani wanda zai yi mulki na gaskiya da izinin Allah.

Mulki lamari ne na Allah saboda, saboda haka duk wanda zai yi jayayya tamkar da Allah zai yi.  Duk wani tsafi da kashe jarirai da surkulle, wallahi ba zai hana mai gaskiya samun mulki ba, sai dai ƙarfin Allah kaɗai zai hana shi wucewa. Amma da izinin Allah, adalci da gaskiya zai tabbata.
Wassalam.

Saƙo daga Ahmad Musa, 07041094323.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *