Wasiƙu

Tarbiyyar ’ya’ya mata: Zuwa ga iyaye…

Wannan wani babban al’amari ne da ya tunkaro gidajenmu, wanda ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen tarbiya da addu’a ga ’ya’yansu, musamman ’ya’ya mata.

Ita karuwar gida ba a gidan karuwai ta ke ba, ba kuma zaman kanta take yi ba, a’a hasalima yawancinsu a gaban iyayensu suke, kodai suna jami’a, suna kwana a can ko kuma suna gidan iyayensu.

A baya idan ka ji an ce wance karuwa ce, to za ka same ta a bariki tana sharholiyar ta, ko dai tana shan taba ko wiwi, amman na yanzu cikin zubin ƙarshen zamani, ‘yan mata ne na gida matsakaita waɗanda ba su wuce shekaru 17 zuwa 25 suke zama karuwai.

Yarinya ce za ka ganta Kamila da shigan kamala, babu alaman iskanci tattare da ita, amman ta zubar da kanta, ana lalata da ita a lungun unguwarsu, wata a Hotal, wata a shago, wata a mota, wata a ɗakin uwarta, wata a ɗakin gayu da ke Off Campus.

Wata karuwar gidan kuma yarinya ce qarama ‘yar shekara 14-17 za ta sanya kayan makaranta na Boko ko Islamiyya, amma ba za ta ƙarasa makarantar ba, sai dai ta je a yi zina da ita, ta dawo gidansu ta kwana.

Abin haushi da takaici, wallahi da yawan waxannan yara babu alaman yunwa tattare dasu, kuɗin da ake ba su da yawansu idan ka ga suturar da ke jikinsu, kai ka san sun fi ƙarfin wannan kuɗin.

Abokanmu maza su ke jefa ƙannenmu mata a irin wannan harkar, da zarar sun ga yarinya ta taso, za ka ji suna ce mata ‘yar shila, kamar wata tsuntsuwa, suna zuga ta akan ta yarda tana da kyau, daga nan su ƙulla alaƙa ta hanyar cusa musu ƙawaye karuwan gidan. Ita wannan yarinyar karuwan gidan, a zahiri kamila ce domin ko yan unguwarsu da yawa basu san tana yi ba, saboda yanayin shigarta na kamala.

Wallahi munin karuwancin gida ya fi na karuwa kilaki mai zaman kanta. Domin da dama sukan je gidan miji da ‘ya’yan wasu, saboda sukan yi ciki a layi ba tare da iyayensu sun sani ba. Mafi yawa daga cikinsu ko da sun yi aure matuqar sun saba kwanciya da mazaje da yawa, ba su iya jure zama da miji ɗaya.

Mafita a nan ita ce;

  1. Idan kana da ’ya ko qanwa ko dai wata mace da kake da iko a kanta, ka tabbatar kana lura da mu’amalarta, suturar da take sanyawa shin kai ka saya mata? Wayar da take riqewa shin kai ka saya? Turarenta da mai shin kai ka saya? Rashin kulawa da wasu buƙatun waɗannan yara da iyaye ke yi, musamman kuɗin kashewa da sayen Data na waya ko ita wayar kanta yakan jefa su wannan harkan.
  2. Dole iyaye su dage da nema wa ‘ya’yansu shiriyar Allah, domin shi ke shiryar da wanda ya so.
  3. Dole ne iyayen da suka saki layin iyaye da kakanni wajen tarbiyyan ‘ya’ya su koma hakan, domin zai yi wuya a baya ka samu yarinya ba a san ina ta ke zuwa ba kuma da su waye ta ke alaƙa kuma waye mai zuwa wajenta, amma na yanzu sun waye za ka ga yarinya har gidansu ta zo da gaye, sai ki ji “Mum ga friend ɗina na School”, Hmm, abu gwanin ban takaici.
  4. Dole iyaye su rage tsangwama, sannan kuma su sanyawa ’ya’yansu wadatar zuciya da nuna musu Allah ke komai, su kuma riƙe mutuncinsu.
  5. A yi ƙoƙari wajen nuna wa yara dogaro da kai, ta hanyar koya musu sana’o’in hannu.

Ubangiji Allah mu ke roƙo ya kare mu daga sharrin zamani, ya kare mana ’yan uwanmu mata daga jin huɗubar Shaidan, duniya da lahira.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUHAMMAD MUSA, 08168716583.

Koyar da ilimin jima’i a makarantu

Yanzu dai ta tabbata, ma’aikatar ilimi ta ƙasa ta bai wa hukumar kula da shirya jadawalin koyarwa a makarantu ta NERDC ta cire duk wani abu da ya shafi ɓangaren koyar da ilimin jima’i a makarantun ƙasar nan. Matakin da qungiyoyin sa kai na al’umma su 54 suka haɗu wajen ƙalubalantar wannan mataki na Gwamnatin Tarayya, bisa hujjar cewa hakan zai iya dawo da hannun agogo baya, a yaƙin da ake yi da yaɗuwar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

Masu goyon bayan wannan tsarin na ganin koyar da yara sanin ilimin jima’i zai taimaka musu wajen sanin mai ya kamata su yi a lokacin da wani babba ya afka musu da nufin fyaɗe ko masu lalata da ƙananan yara, daga cikin abokan karatu, gurɓatattun da wasu makusanta na gida ko na anguwa, musamman yadda cutar HIV mai karya garkuwar jiki take yaɗuwa, da sauran cututtuka da ake samu daga jima’i marar tsafta.

Har wa yau kuma, ana danganta matsalolin da yara mata da ke shekarun fara al’ada suke fuskanta, samun shigar cikin da ba a shirya shigarsa ba, ta dalilin fyaɗe ko yaudarar wasu maza, da kuma damuwoyin da ake samu yayin zubar da ciki ko amfani da magungunan hana ɗaukar ciki, kan rashin samun ilimin jima’i da wuri, da ba su shawarwarin da ya dace a kan lokaci.

Tun farkon shigo da wannan tsari kimanin shekaru 20 da suka gabata a makarantun Nijeriya, ya sha suka sosai a wajen malaman addini, masana tarbiyya da iyaye, waɗanda ke ganin illar yin hakan ga gyaruwar tarbiyyar ƙananan yara da ke tasowa da tunanin gwada duk wani abu da suke ji ko gani, domin tabbatar da yadda yake, ba tare da sun san illoli ko rashin dacewar hakan ba.

Lallai dole malamai da masu nazari kan harkokin ilimi su koka ga irin wannan tsari na koyarwa da bai dace da ƙananan yara da ba su balaga ba, ko kuma suke da qananan shekaru, domin tasirin da hakan ke da shi ga tarbiyyarsu da tunanin su. Wannan tattaunawa ba kasafai iyaye ke zama su yi shi da yara ba, saboda kunya da al’ada. Kamar yadda mahaifiyar Zainul Abideen ta kasa natsuwa ta saurari tambayoyin da ɗanta yake yi wa babansa ma. Fahimtarta tayi daidai da tawa, inda muke ganin wannan koyarwa ba ta dace da ƙananan yara irin sa ba.

Ko da yake mun taso a al’adance a nan qasar Hausa sai yaro ya girma har ya kusa balaga ne sannan yake fara sanin wasu abubuwan, kafin wani yayanshi ko malaminsa na Islamiyya ya fara koya masa abubuwan da, suka wajaba a kansa na game da ayyukan ibada da zaman aure. Haka ita ma mace daga lokacin da ta fara jinin al’ada, a lokacin ne mahaifiyarta ko qanwar mahaifiyar ta ke sanar da ita wasu abubuwa da ya kamata ta kula da su, da kuma a makaranta wajen karatun ilimin addini, inda malaman fiqhu suka yi bayani dalla dalla, game da hukuncin addinin Musulunci a game da waɗannan muhimman batutuwa da suka shafi al’ada, balaga, jima’i da zamantakewar aure.

Yadda rayuwa ta canza a halin da ake ciki, abubuwa na ilimomi na nan birjik a kafafen sadarwa na zamani, wanda ba ka buqatar zaunar da yaro ka koya masa wani abu, sai dai ƙoƙarinsa na sa ido da tarbiyyar da shi a kan tsarin addini da halayen ƙwarai, don kada ya yi amfani da ilimin da yake gani a yanar gizo ta inda bai dace ba.

Wasiƙa daga MUHAMMAD AUWAL MUSA (Ya Muha), 08062327373.

Leave a Reply