WASIƘU: Illar cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a (II)

  • Yadda tsadar rayuwa ta jefa ’yan Nijeriya cikin ƙunci

A wannan makon zan ci gaba da yin bayanin da na soma kan wannan maudu’i namu abin dubawa, kamar yadda yake a sama. Domin su kalaman cusa ƙiyayya suna da ɓangarori daban-daban, kuma kowa da yadda yake kallon nasa ɓangaren. Inda wani yana ganin shi ai ba yana yi ba ne don ya muzguna wa wani, don haka idan aka nemi a hana shi sai ya ga tamkar an tauye masa haƙƙi ne na faɗin albarkacin baki.

Haka kuma wasu na ganin irin waɗannan kalamai da suke furtawa, kalamai ne da kawai suna yin su don su huce zuciyarsu game da wani abu da ya ɓata masu rai. Kamar yadda wasu kuma, musamman a ɓangaren adini suke yi don su nuna duk wata fahimta da ba tasu ba, to ba ta bisa kan hanya, don haka za su yi ta fura kalaman da dole sai sun tunzura wanda abin ya shafa.

Wannanan ne ya sa a makon da ya gabata muke maganar cewa irin waɗannan kalamai ba su dace ba, domin a cikin addinin ma an yi maganar cewa babu tilasta wa wani ya bi abin da kake yi. Don haka duk irin waɗannan kalamai ba su dace ba, kuma wajibi ne duk wani mai yinsu ya kiyaye, sannan kuma ita Hukuma, wajibinta ne ta ga cewa al’ummarta sun zauna lafiya ta hanyar yi ma tukka hanci.

A kwanakin baya gwamnatin tarayya, ta bakin Maitamakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo ta bayyana ɗaukar matakin cewa za ta sanya irin waɗannan kalamai na cusa ƙiyayya a cikin aikin ta’addanci, sannan za a hukunta masu furta su a tsarin nan na yaƙi da ta’addanci.

Ita dai gwamnatin tarayya, ta hannun Mataimakin shugaban ƙasar, wanda kuma ƙwararren Lauya ne, ta yi wannan tunanin ɗaukar matakin ne bisa la’akari da cewa irin waɗannan kalamai na iya jefa ƙasar cikin wani mummunan hali na yaƙin cikin gida da zubar da jini ba bisa ƙa’ida ba, tare da cusa gabar da ba a san inda za ta ƙare ba.

Kusan duk wani rikici da ke faruwa a tsakanin al’umma, na addini ne, siyasa ce, ƙabilanci ko wata fahimta, to duk yana samo asali ne daga wasu kalamai da ake furtawa, waɗanda wasu lokuta ma daga nan inda ake furta waɗannan kalaman ne ake wucewa wajen tashin hankali, a auka wa wanda bai ji ba, bai gani ba. Wanda kuma a wasu lokuta jami’an tsaro kan bi diddigi su kamo waɗanda ake zarginsu da furta irin waɗannan kalaman.

Shi wannan abu na kalaman cusa ƙiyayye da wasu suka mayar da shi hanyar cin abinci, ba wani abui ne yake jawowa ba, illa cin mutunci, tozartawa, cin zarafi, tunzura mutum ko tunzura gungun mutane su ɗauki matakin da bai dace ba a kan wani ko wasu, ta hanyar hayaniya da zubar da jini.

Saboda kamalaman cusa ƙiyayya mayan makamai ne na samar da hargitsi ko riciki a tsakanin jama’a, wanda kuma yana wuyar gwamnati ta bi duk hanyoyin da za ta bi don ganin haka bai auku ba. Su kuma al’umma, musamman shugabannin addini, wajibinsu su kauce wa irin waɗannan kalamai.

Saboda haka idan aka yi la’akari da irin waɗannan abubuwa, zai zama wajibin kowace gwamnati ce ta ga cewa ta ɗauki duk matakin da ya wajaba don tsaron dukiya da rayukan al’ummarta, wanda kuma ɗaukar matakin haramta irin waɗannan kalamai, tare da hukunci mai tsanani ga duk wasu furtasu, wani abu ne da za a iya cewa ya wajaba.

Rashin ɗaukar matakin gaggawa kan irin waɗannan abubuwa, to zai iya ƙasa ga wani irin yanayin da ba a san inda zai ƙare ba. Domin babu wani abu da ke sa ƙasa da al’ummarta su koma baya kamar yaqi, kuma shi wannan abu na kalaman cusa ƙiyayya, ba abin da yake haddasawa kamar yaƙi a tsakanin al’umma.

Don haka ashe ya zama wajibi ga gwamnati ta ɗauki irin matakin da ta ɗauka na nuna ba sani ba sabo kan duk wani aka samu yana furta irin waɗannan kalamai.

Saboda haka don Nijeriya ta ɗauki matakin hukunta masu irin waɗannan kalamai, ba ita ce farau ba, domin ƙasashe da dama sun riga sun ɗauka tuntuni. Misali, ƙasar Belgium ta yi wannan doka a 1981, Brazil a 1988, Canada a 1990. Haka ma ƙasshen Faransa, Germany, Japan, Afrika ta Kudu, Denmark, Finland da dai sauran ƙasshen da dama, inda ma a ƙasar Canada aka sanya cewa duk wanda aka kama da laifin furta kalaman cusa ƙiyayya, zai kwashe shekara biyar a gida kaso.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun injiniyan Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Yadda tsadar rayuwa ta jefa ’yan Nijeriya cikin ƙunci

Assalamu alaikum. Kamar dai yadda muka sani ne cewa, a halin yanzu ba a tava shiga irin mawuyancin hali ba a ƙasar nan kamar irin wadda ake ciki yanzu.

Masana kan tattalin arziki sun bayyana cewa, a halin da ake ciki a yanzu tattalin arzikin ƙasar nan bai hau kan farkin gyaruwa ba, duba da cewa gwamnati bata hau kan turbar da ta dace ta farfaɗo da tattalin arziki ba.

Haka zalika masana sun ƙara da cewa, sun bayyana cewa, al’ummar ƙasar nan suna cikin matsakaicin talauci, hakan tasa suka ƙara shiga cikin matsin rayuwar da suke ciki a yanzu.

Mazauna ƙasar nan dai na kokawa dangane da matsin tattalin arzikin da ƙasar nan yake fama dashi, ta inda al’umma da dama da ada suke cin abinci sau uku, daga bisani kuma ya dawo ci sau biyu, yayin da waɗanda suke ci sau biyu suka dawo sau ɗaya abun da ake kira da tazarce , wasu kuwa sai su yini, su kwana basu ga ko kanzo ba.

A gefe ɗaya kuwa ’yan kasuwa na kokawa kan rashin kasuwa kasancewar idan sun kasa kayayyaki ba ko yaushe suke samu masu saya ba, yadda wataran sai su yini ko sisin kobo ba a sayi ba.

A hannu guda kuma mutane na kokawa kan yadda Nijeriya za ta ci gaba da zama cikin irin wannan hali, domin talata kawo yanzu bai ci ribar dimukuraɗiyyar ba. Allaha ya sa mu dace, Ameen. Wassalam.

Daga Khadija Alhasan, 09070905293.