WASIƘU: Lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya (1)

*Dogaro da lissafin Miladiyya

Assalamu alaikum. Da fatan kowa yana lafiya! Ga duk mai bibiyar al’amuran da suka shafi shafin yanar gizo, ko kuma in ce harkar yaɗa labarai a ƙasar nan ya san yadda a ’yan watannin nan ake yawan samun koke-koken game da yadda wasu Malaman Jami’o’i ke lalata da ɗalibansu don su ba da maki, ko kuma don a kai su inda ba su kai ba a harkar jarabawa.

Ko ba a ce komai ba, wannan wani mummunan abu ne da za a iya cewa bai kama da hakali ba, ko kuma mu ce wani abu ne da ya zama bala’i wanda idan ba a yi hankali ba zai iya zama wata annoba da za ta taɓa tarbiyyar ’ya’yanmu da kuma kawo mummunan nakasu a harkar ilimi a ƙasar nan.

Irin wannan abu da waɗannan ɓata-garin Malamai suke yi, wani abu ne da aka jima ana yinsa, sai dai bai zama ruwan dare ba kamar a ’yan watannin nan, inda ake kamawa, tare da ɗaukar mataki a wasu makarantu. Amma wasu kam har yanzu suna nan suna cin karensu babu babbaka.

Sai dai duk da haka za a iya cewa ana samun sauƙi, domin an saba idan irin waɗannan abubuwa suna faruwa ba a ɗaukar wani mataki a kai, bilhasali ma idan wata ɗaliba ta kuskura ta kai ƙarar irin wannan cin zarafi, to kashinta ya bushe, domin Malaman za su haɗe ma ta kai ne, su gaba-gaba har wajen Hukumar makarantar su qaryata ta, a ƙarshe a ce ita ce ba ta da gaskiya.

To amma a ’yan watannin nan abin ya zama ba haka ba, domin duk yarinyar da ta kai irin wannan ƙara, to Hukumar makarantar tana ɗaukar matakin da ya dace wajen hukunta irin waɗannan mugayen Malaman.

Akwai musalai da dama inda aka ɗauki irin wannan mataki. Misali, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, an kama wani Malami wanda ya yi fice a irin wannan aika-aikar, inda kuma bayan bincike ta hanyar wani ƙaƙƙarfan kwamiti, aka sallame shi.

Amma sai dai abin takaici, bayan ’yan watanni sai aka ji wannan Malami ya samu aiki a Jami’ar jihar Kaduna. Kodayake na ga an sanya batun a gaba a yanar ginzo, inda har na ba cin karo da wani martini na Gwamna Malam Nasir El-rufai, inda yin godiya game da wannan nusarwa da aka yi masu, kuma ya ce Kwamishina Ilimi da Kwamishinan shari’a za su bi lamarin.

Haka zalika, a Jami’ar Tarayya da ke garin Dutsin-ma ta Jihar Katsina nan ma ana yawan samun irin waɗanda matsalolin, domin akwai wata ɗalibar da ke gaya min cewa, wasu daga ciki Malaman jami’ar, kusan kashi saba’in bisa ɗari, suna neman ɗalibansu, idan kuma ɗaliban suka ƙi ba su haɗin kai, sai su riƙe su a jarabawa.

Haka kuma a jihar Ekiti, Hukumar gudanarwar Jami’ar jihar ta kori wani Malamin Jami’ar mai suna Olola Aduwo, korar kuma irin korar da Marigayi Musa Dankwaro ke faɗi, ‘Ba Fansho Ba Garatuti.’ Korar da ta fara aiki daga watan Oktobar da ya gaba sakamakon kama shi dumu-dumu a irin wannan badala.

Irin waɗannan misalai suna da yawa, waɗanda kuma na tabbata ana ɗaukarsu ne don ya zama darasi ga wasu, duk da yake wasu dai abin ya zama masu jiki, amma dai idan kare na yawo, sanda na yawo, wata rana za a haɗu.

Kamar yadda na faɗa a sama, abin farin cikin shi ne yadda Hukumomi a Jami’o’i da gwamnatoci ke abin da muhimman a yanzu fiye da a da, wanda ɗaliba ba ta da wani abin yi, ko dai ta ba da kai bori ya hau ko kuma ta rasa karatun.

Wani abin farin ciki shi ne a kwanakin baya Majalisar Dattawan ƙasar nan ta gabatar da wani ƙuduri mai zafin gaske da zai daƙile yawaitar irin wannan cin zarafin da ake yi wa mata a Jami’o’i.

Wannan dokar da za ta taimaka wajen daƙile yawaitar wannan cin zarafin mata ta nau’o’i daban-daban, walau ko ta tursasa musu a yi zina da su don a ba su maki, ko karɓar kuɗaɗensu, ko wasu hanyoyi, idan an samu nasarar dokar, za ta taimaka wajen wa ɗalibai a manyan makarantun da suke ƙasar nan.

Wannan dokar tana zuwa ne a daidai lokacin da ƙorafe-ƙorafe ya yi yawa game da wannan lamari, wanda kuma kowa na ammannar cewa idan har aka tabbatar da ita, to za ta taimakawa ’ya’yan jama’a.

A cikin tanadin wannan doka da Majalisar ta gabatar, an ware wa’adin shekaru har 14 a kurkuku ga duk Malamin da aka cafke yana lalata da wata ɗaliba a duk faɗin qasar nan, ba tare da wani zaɓi na biyu ba.

Ƙudurin wanda ya zarce karatu na ɗaya da na biyu a Majalisar Dattawan, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya gabatar da shi, da fatan idan ya zama doka zai kawo ƙarshen wannan cin zarafin.

Daga Mahdi Musa Muhammad, marubuci kuma Ƙaramin Editan a jaridar Blueprint Manhaja – 07066778190. Haka kuma ga duk mai son tofa albarkacin bakinsa, zai iya aiko da saƙo ta [email protected] ko [email protected]

Dogaro da lissafin Miladiyya

An ce rashin uwa mai sa a yi uwar ɗaki. Musulumai muna da ta mu shekara ta Hijira mai watanni 12. Ashe dogaro da shekara ta nasara Miladiyya za mu iya kallon hakan ta fuskoki kamar haka. Rashin maida hankali wanda sakacinmu musulmai ne.

Za a samu mutum musulmi ya haddace dukkanin watannin Miladiyya amma idan an juyo ga watanni 12 na Hijira a nan ne za a sha mamaki. Sai masu kusanci da karatu ne kaɗai ke iya kawo jerin sunayen Hijira daga Muharram zuwa Zul-Hijja.

Ina fatan mu musulmai mu qara kula. Duk abinda ya shafi karatu sai masanansa. Na yi wannan ’yar nusarwa domin mu rinƙa kallon namu matsalolin wanda a yau hatta lissafi na nisabi da ƙididdije lukutan salloli biyar muna samun bambanci nan da cen. Miladiyya dai lalura ce amma gane hakan sai mun kusanci karatu.

Na dau Miladiyya a matsayin lalura a rayuwa amma ban hana kowa tasa fahimtai ba.  Allah ka kawo ma mu ɗauki da mafita a rayuwar mu har zuwa matabbata, Amin.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa – 07066434519, 08080140820