WASIƘU: Yawan mace-macen aure – Rashin haƙuri ko rashin tarbiyya?

*Ko mun san muhimmancin sada zumunci?

Assalamu alaikum. Da farko dai, sada zumunci shine kyautatawa da jinƙai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk ɓangare ne na sada zumunci. Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga ɗan uwa yayin haɗuwa da gaishe shi da ce masa Yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi. Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da riƙe amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a ɓoye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunci ne.   

Hukuncin sada zumunci:
Wajibi ne Musulmi su sada zumuncin da ke tsakaninsu, kamar yadda shiryarwar Musuluci ta ginu kan haka, Allah Ta’ala Yana cewa, “ka tuna lokacin da muka riƙi alƙawari daga Banu Isra’ila cewa kada su bauta wa kowa sai Allah, kuma su kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci (’yan uwa) da marayu da miskinai, kuma ku gaya wa mutane kyakkyawan zance, kuma ku tsai da Sallah ku bada Zakka, sai kuka juya baya (ga barin wannan umarni), sai ’yan kaɗan ne daga cikinku, kuna masu bijirewa.” Kuma a suratul Baƙara, aya ta 27 Allah Ya fassara fasiƙai a cikin faɗinsa, “su ne masu warware alƙawarin Ubangiji (kan aiko Annabi SAW), bayan ƙarfafa alƙawarin gare su, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (zumunci), kuma suke ɓarna a bayan ƙasa, waɗannan su ne taɓaɓɓu.”

Ma’abuta zumuci:
Su ne duk makusantan mutum (na jini) na kusa ko na nesa, magadansa ne ko ba magada ba, muharramai ne ko ba muharramai ba, masu dangantaka da shi da suka haɗa da kakanni da iyaye da ’ya’ya da jikoki, ’yan uwa maza ko mata kanne da yayye da ’ya’yansu da ’yan uwan uba da na uwa. Idan muka faɗaɗa ma’anar zumunci zuwa ga ’yan uwantakar Musulunci da bada haƙƙi ga ma’abutansa, to kai-tsaye, aya ta 36 a Suratun-Nisa’i, za ta yi mana jagoranci ga raba ma’abuta haƙƙin kyautatawa zuwa gida uku, inda Allah Maɗaukaki Yake cewa, “kuma ku bauta wa Allah, kada ku haɗa wani da shi a cikin bauta (shirka), kuma ku kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci da marayu da miskinai da makwabci ma’abucin zumunci da makwabci manisanci da aboki a gefe da ɗan tafarki da bayinku. Haƙiƙa Ubangiji ba Ya son wanda ya kasance mai taƙama, mai yawan alfahari.”

Bisa koyarwar wannan aya, za mu iya raba ma’abuta haƙƙin a kyautata musu zuwa gida uku:
a) Mutum mai haƙƙi uku: ɗan uwa na jini Musulmi kuma makwabci.
b) Mautum mai haƙƙi biyu: Musulmi kuma maƙwabci.
c) Mutum mai haƙƙi zaya: maƙwabci a gida ko a kasuwa ko abokin tafiya da ba Musulmi ba.

Falalar sada zumunci:
Falalar sada zumunci ba za ta kayyadu ba, sai dai kawai a faɗi kaɗan daga ciki:

  1. Tsawaitar rayuwa.
  2. Wadatar zuciya.
  3. Bunƙasar dangi.
  4. Tsallake Siradi cikin sauƙi.
  5. Samun yardar Allah.
  6. Samun haɗin kai.
  7. Samun shiga Aljanna da sauransu.

Uƙubar yanke zumunta:
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, shi ne abin da za mu iya cewa, saboda abin da ya samu zumunci na ɓalɓalcewa, babu zumunci, ɗan uwa ya ga ɗan uwansa, kowa ya shige, saboda rashin sani, ko a kan sani. Ba a zumunci, mai kuɗi don girman kai da ganin sai dai shi a zo masa, talaka kuma don tsoron wulaƙanci, talaka da talaka kuma don tsoron kada ya ɗora wa ɗan uwansa nauyi.

Ayoyi da Hadisai da dama, sun ja kunne kan yanke zumunci. Ma’aiki (SAWW) ya ce, “mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba.”

Hanyoyin sada zumunci:
Ana sada zumunci ne ta hanyoyi da dama, kamar tattaki zuwa wurin ’yan uwa ko wasiƙa ko wayar sadarwa ko saƙon baka (a aika gare) ko shirya tarurrukan taya farin ciki ko jajanta wa wani.

Allah Ya inganta zumuncin da ke tsakanin Musulmi, ya kuma ba mu damar cigaba da sada zumunci da ’yan uwanmu, Ilahee Ameen.

Wassalam.
Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Yawan mace-macen aure: Rashin haƙuri ko rashin tarbiyya?

Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a ƙasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na karewa da saki.

Shin ko me ke janyo wannan matsala? Wane irin tasirin ta ke yi a kan zamantakewar al’umma? Me ya kamata a yi don a rage matsalar?

An yi kira ga gwamnati ta sanya darasin ilimin aure a cikin manhajar karatun sakandare da nufin rage yawan mace-macen aure a cikin al’umma.

Mace-macen aure matsala ne da ya yawaita a ƙasar Hausa. An yi ittifakin cewa jihar Kaduna na da yawan zawarawa manya da ƙananan yara.
Ga wasu daga cikin abubuwan da ake ganin suna haifar da matsalar:

  1. Jahilci: Matsala ta farko da take jawo macen aure a ƙasar Hausa a wannan zamani ita ce jahilci da yawan mutanenmu, musamman mutanen, mun jahilci mene ne aure, ma’anarsa da kuma a Addinance. Da yawan matasa da suke aure a yanzu yawancin su basu san ma’anar aure ba, ba su san ƙa’idojin aure ba, basu san hukunce-hukuncen aure ba, kai wallahi wasu ma ba su san ya ake yin wankan Janaba ba, amma a haka suke zuwa neman aure kuma a ba su.
  2. Kwaɗayi: Hausawa dai suna cewa, “idan har da kwaɗayi, to da wulaƙanci”, kuma kowa ya hau motar kwaɗayi to zai sauka a tashar wulaƙanci. sannan ƙuda wurin kwaɗayi yake mutuwa. Da yawan mace-macen auren da ke faruwa a ƙasar Hausa suna biyo bayan kwaɗayi ne da a’auratan suke sawa a cikin kwanciyarsu tun kafin su yi aure.
  3. Auren dole na daga cikin wuraren da ke kawo yawan mace-macen aure musamman a ƙasar Hausa inda abin ya zamo ruwan dare.
  4. Auren Zumunci idan ya yi kyau ya fi komai daɗi, idan kuma ya ɓaci ya fi komai muni. Irin wannan aure kan yi ƙarko ne kawai idan ma’auratan ne suka haɗa kansu.
  5. Auren Sha’awa: Auren sha’awa dai shi ne mutum ya yi aure domin kyawun jiki ko surar ɗan uwansa, illar irin wannan auren shi ne; da zarar waɗannan suffofi da aka yi auren domin su suka gushe, to shikenan matsala za ta fara afkuwa a auren, daga nan sai rabuwa.

Saƙo daga Malam Sa’id, 09070905293.