Wasu cibiyoyin ƙasar Sin sun tallafa wa makarantun firamare a Habasha da injunan samar da tsaftataccen ruwan sha

Daga CMG HAUSA

Wasu cibiyoyin ƙasar Sin 4, sun tallafawa wasu makarantun firamare dake yankin SNNP na kudancin ƙasar Habasha, da injunan samar da tsaftataccen ruwan sha.

Wata sanarwar da cibiyoyin suka gabatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, cewar cibiyar nazarin bunƙasa jagoranci ta Sin da Afirka ko (CALDI) ta jami’ar Tsinghua ta ƙasar Sin, da kamfanin HurRain NanoTech, da asusun raya karkara na ƙasar Sin (CFRD), da asusun fama da talauci ta ƙasar Sin, a matsayin sassan da suka yi haɗin gwiwar ba da taimakon.
Makarantun da suka samu tallafin kuwa sun haɗa da firamaren Key-Afer, da ta Tulungo, da ta Sitimba, da makarantar Turmi and Demeka. An yi ƙiyasin ɗalibai kimamin 2,106 a waɗannan makarantu za su ci gajiya daga ruwa mai tsafta da aikin ya samar.

Manyan jami’an da suka halarci bikin miƙa na’urorin sun haɗa da uwar gidan shugaban kasar Habasha Roman Tesfaye, da wakilan hukumomin yankin, da suka haɗa da shugaban sashen ilimi na Omo ta kudu Weli Haile, da wakilin ɓangaren Sin.

Mai fassara: Saminu Hassan