Wasu dabarun yi wa yara tarbiyya

Daga ABDULLAHI YAHAYA

‘Ya’yanmu amana ce da Allah ya ba mu, kula da su da kuma karkatar da su zuwa ga hanya madaidaiciya haƙƙi ne da ya rataya kan mu. Ba wa yara tarbiyya sha’ani ne mai matuƙar muhimmanci a addini, domin Allah zai tambaye mu yadda mu ka ba wa amanar da ya ba mu tarbiyya. A wannan zamani da mu ke ciki, da iyaye za su dage wurin bai wa ‘ya’yansu tarbiyya, da tabbas an samu sauƙin tashin hankula da ya yi katutu a cikin mu.

Sai dai tuni iyaye suka wurgar da koyarwa addinin Musulunci game da tarbiyya, suka ɗauki hanyar da sheɗan ya nuna masu a matsayin wayewa. Wannan ya sa suke bar wa ‘ya’yansu ragamar rayuwarsu a hannunsu, su yi duk abin da suke so. Wannan ne zai ba wa sheɗan damar ɗaukar su ya kai ga hanyar da za ta kai su ga nadama.

Iyaye ku ji tsoron Allah, ku ɗora ‘ya’yanku bisa tafarki mai kyau ko da kuwa ba shi suke so ba. Ku nemi sanin hanyoyi da za ku bi don ba wa yaranku tarbiyya cikin sauƙi. Ga wasu daga cikin hanyoyin da za ku bi don sauƙaƙa tarbiyya:

1: Ware masu lokacin wasanni: Kada ka takura yaro ka hana shi yin wasa.Wasanni na kara bunƙasa ƙwaƙwalwar yara. Don haka a riƙa barin yara suna samun lokacin yi wasannin. Wanda ba zai cutar da su ba.

Yara suna son su riƙa wasa da iyayensu a lokacin da suke wasannin su na tsalle-tsalle da guje-guje.
Yana da kyau iyayen suna samun lokaci wajen maida kansu tamkar yara wajen yin wasanni da ‘ya’yansu, hakan na sa iyayen su fahimci basira da kuma hazaƙa dama ɗabi’un yaransu.

2: Zaman hira: Yana da kyau iyaye su riƙa samun lokaci suna hira da ‘ya’yansu. Hakan zai sa ka fahimci irin basirar da yaro yake da shi a lokacin tattaunawar ta ku.

Haka nan kada ka hana yaro yawan tambaya, sai dai ka riƙa ɗora shi akan yadda ya dace ya yi tambayar. Ka kuma riqa amsa duk wani tambayar da yaro ya ma ka yadda zai iya fahimtar ka daidai da irin hankalinsa.

3: Kula Da Basira: Ka kula da basirar da kowanne yaronka yake da shi domin ganin ka ƙarfafa masa wannan ɓangaren. Wasu yaran tun suna da ƙarancin shekaru ake iya fahimtar irin basirar da Allah Ya yi masu. Ta hakan ne za a samu dama da lokacin taimaka masu wajen cinma wannan burin nasu.

Allah Ya shirya mana zuriya akan hanya madaidaiciya.