Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ce wasu jihohin da ba su da ƙarfin tattalin arziki za su shiga tasku idan aka amince da ƙudurorin haraji da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika majalisa.
“Don haka dole a nazarci ƙudurorin cikin tsanaki saboda kar mu cuci kanmu,” in ji shi a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Talata.
Ya ƙara da cewa, “a cikin ƙudurorin akwai abubuwa masu kyau, akwai kuma marasa kyau, wannan ya sa muke ƙara nazartar abubuwan da ke ciki domin ba mutanenmu shawara kan abin da ya kamata.”
Lawal ya ƙara da cewa jihohi da dama ba za su iya biyan albashin naira 70,000 matuƙar an tabbatar da gyare-gyaren da ke cikin ƙudurorin.
“Gyare-gyare na da kyau, amma yana da kyau mu guji gaggawa domin gudun yin da-na-sani daga bisani.”
Dokar gyaran ƙudirin harajin dai tana fuskantar suka daga ɓangarori daban-daban na al’ummar Nijeriya, wanda wasu ke ganin zai kassara Arewacin ƙasar da kuma ƙara ta’azzara ƙuncin rayuwar da ake ciki.