“Ina jin daɗi idan na ga ɗaliban da na koyar sun zama wasu manya”
Daga: ABUBAKAR A BOLARI, Gombe
Mace ‘yar Scout mai manyan muƙamai a Arewacin Najeriya, Hajiya Hauwa Isiyaku mamba ce a ƙungiyar Scout ta Najeriya kuma jajircecciyar mace ce a fagen rayuwa. A duk faɗin Arewacin Najeriya, babu wata mace da take da irin muƙaminta a Scout, baya ga samun Wood Badge. Ta halarci kwasa-kwasai da dama kan harkar Scout, Baya ga aikin Scout, Hajiya Hauwa kuma ƴar kasuwa ce, ma’aikaciyar gwamnati, kuma tana da kamfani mai suna ‘2Able Graphics and Catering Serɓices’ da ke unguwar Zari’a Road a birnin Kano. A hirarta da shafin Gimbiya na Jaridar Manhaja, Hajiya Hauwa ta bayyana cikakken tarihin rayuwarta da gwagwarmayarta. Ga yadda hirar ta kasance:
MANHAJA: Za mu so jin cikakken sunanki, ko wacce ce Hajiya Hauwa Isiyaku?
HAJIYA HAUWA: Assalamu alaikum. Da farko dai, sunana Hajiya Hauwa Isiyaku. Ni haifaffiyar garin Kano ce, na yi karatuna na firamare da na Islamiyya a Unguwa Uku, cikin ƙwaryar Kano, a yankin ƙaramar Hukumar Tarauni.
Bayan haka, na yi karatun gaba da firamare a makarantar ‘yan mata ta Sule Tankarkar da ke Jihar Jigawa. Na kuma yi karatun kwalejin ilimi a Jihar Kano. Ni ƴar kasuwa ce, kuma ma’aikaciyar gwamnati, sannan kuma mamallakiyar kamfanin ‘2Able Graphics and Catering Serɓices’ da ke unguwar Zari’a Road, Kano.
Bayan duk wannan karatu da kamfanin ‘2Able Graphics’, ko kina wata ƙungiya?
Eh, ni mamba ce a ƙungiyar Scout ta Najeriya, ina riƙe da muƙami mai girma a matakin jiha da ƙasa. A kwanannan na samu horo a Jihar Kaduna, wanda shi ne matakin ƙololuwar horo a ƙungiyar, wato Leader Training (LT) wanda ake iya kwatantawa da PhD a jami’a.
Ko yaushe ki ka fara aiki?
Na fara aikin koyarwa a wata makarantar kuɗi da ke CBN ƙuarters mai suna New Era Nursery and Primary School. Na yi aiki da su tsawon shekara biyu, sannan na koma wata makaranta mai suna Friendship International School da ke unguwoyi uku, layin Yarbawa. Bayan haka, na yi aiki a wata NGO a cikin asibitin Malam Aminu Kano, wato IHɓN (Institute of Human ɓirology Nigeria), inda na yi aiki a matsayin mai sa kai (ɓolunteer) a sashin kula da marasa lafiya a gida (Home Based Care).
Daga nan kuma, na shiga ƙungiyar Red Cross, wato ƙungiyar bayar da agajin gaggawa a Kano. Har yanzu ina cikinta. Bayan na bar IHɓN, na koma koyarwa a ma’aikatar ilimi, wato KSSSMB (Kano State Senior Secondary Management Board), ina matsayin malamar makaranta. Duk da waɗannan ayyuka, ina ci gaba da sana’ar kasuwanci, ina sayar da kayan sawa da na amfanin gida. Haka kuma, ina rubuce-rubuce na littattafai masu ma’ana, amma rashin tallafi ya hana ni bugawa. ɗaya daga cikin littattafaina mai suna ‘Matsalolin Auren Dole’ yana magana ne kan tilasta wa ‘ya’ya mata aure, wanda nake ganin cin zarafi ne. Na rubuta wani fim mai suna ‘Ra’ayi ko Sunna’, wanda yana magana ne kan yadda wasu maza ke musguna wa mata idan suka sake su ta hanyar ƙin bayar da kuɗin ciyarwa ga yaran da suka haifa tare da su.
Ya ki ka kafa kamfanin ‘2Able Graphics’?
A cikin waɗannan ayyuka da rubuce-rubuce na neman kuɗi, sai muka haɗa gwiwa da Ibrahim Isiyaku, wanda aka fi sani da ‘2Able Graphics’, muka buɗe shago tare. Muna aikin bugawa da zane-zane a cikin shagon, wanda ake kira 2Able Graphics. Ni na zama manajan darakta na wannan shagon da ke Unguwa Uku, layin Mai Nono, a ƙaramar Hukumar Tarauni. Allah ya yi wa Ibrahim rasuwa, kuma yanzu ni ce ke tafiyar da dukkan harkokin shagon, ciki har da yin kwangilar abincin biki da sanya rubutu da ado a riguna, kamar T-shirts.
Kin halarci wasu kwasa-kwasai na musamman a ƙungiyar Scout?
Gaskiya ne, na halarci kwasa-kwasai masu muhimmanci a ƙungiyar Scout. Na yi ‘General Information Course’ (G.I.C) da ‘Basic Training Course’ (B.T.C) a Jihar Kogi, a garin Asaya. Bayan haka, na rubuta jarrabawar ƙungiyar Scout mai suna Theory. Na yi wasu kwasa-kwasai na CUBs Scout, wato ɓangaren yara, wanda na yi shi a Jos.
Wanne ci gaba ki ka samu a aikinki?
Alhamdulillah, na samu nasarori da dama, musamman ta sanin jama’a. Ina jin daɗi idan na ga ɗaliban da na koyar sun zama wasu manya. Wannan aiki na Scout kuma ya bani damar ƙara mu’amala da sauran ‘yan Scout na Nijeriya, wanda ya sa na zama mace ta daban a Arewacin Najeriya.
Wanne ƙalubale ki ka fuskanta?
A rayuwa, ba za a rasa ƙalubale ba, amma abu mafi wahala shi ne yadda wasu maza ke amfani da raunin mata wajen cimma buƙatun shaiɗan a wurin aiki. Sukan take gaskiya, musamman idan mace bata biya musu wasu buƙatunsu ba.
A waɗane ƙungiyoyi ki ke ciki baya ga Scout?
Na shiga ƙungiyoyi da dama kamar “Foundation for the Support of Less Priɓilege” da kuma ƙungiyar Matasan Arewa da dai sauransu.
Kin taɓa zuwa wasu ƙasashen waje?
Eh, na ziyarta ƙasashen waje kamar su Kwatano, Ghana, Nijar, Togo, da Dubai. Haka kuma, na zagaya garuruwa da dama a Nijeriya.
Menene burinki a rayuwa?
Buri na shi ne na zama babbar ‘yar kasuwa a Najeriya, sannan in taimaka wa mata ‘yan uwana wajen neman haƙƙinsu da kuma yaƙar lalacewar tarbiyar ‘ya’ya mata.
Wacce sutura tafi burgeki?
Tufafin da ya fi burgeni shi ne doguwar riga mara nauyi da zai rufe sassan jikina yadda duk wanda ya ganni ba zai min kallon banza ba. Haka kuma, nakan yafa gyale domin rufe jikina da kyau.
Wacce shawara za ki bai wa iyaye?
Shawarar da zan ba iyaye musamman mata ita ce, su riƙi addini da kyau, su kuma bai wa ‘ya’yansu wadatar zuci da ilimi, musamman ‘ya’ya mata. Hakan zai ba su damar samun kyakkyawar rayuwa. Kuma, bana goyon bayan a cire yarinya daga makaranta tun tana sakandare a aurar da ita, domin hakan yana haifar da koma baya ga tarbiyar yara.
Mun gode.
Ni ma na gode.
