Daga UNCLE LARABI
To, ban san me zanyi na zama ɗan Kwankwasiyya ba. Na san dai tun 1999 nake son Engr. Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Mun haɗu da shi sau uku kacal ido da ido. Biyu a Rumfa Collage a Shekarar 2001 da kuma sanda ya dawo a shekarar 2011.
Ina son sa, duk wanda ya san ni a zahiri ya san haka. Kuma duk wanda ya san Facebook Page ɗina, wanda aka yi ‘deactiɓate’ dalilin rubutun da na yi akan shi Engr. Rabi’u Kwankwaso da Tinubu da Peter Obi da Atiku mai taken ‘Komai sanyin tuwo ya fi teba!’ shine rubutuna na ƙarshe a fejin da na kwashe shekaru sama da 15 Ina amfani da shi.
Ina da tarin abokai da ‘followers’ a wancan ‘account’ ɗin masu yawan gaske, don na fi da yawan waɗanda suke da ‘followers’ a yanzu yawan ‘followers’. Sunan Facebook Page ɗin Larabi Larabeen.
Na rasa rubuce-rubucena da yawa na littattafaina da rubutun hikimomi da na siyasa da na jaridu da na yi musu suka wallafa. Na rasa hotuna da bidiyo da tarihin tafiye-tafiyena da na yi ƙasashen ƙetare kama daga ƙasashen Afrika zuwa Nahiyar Turai da Saudi Arabia. Na rasa hotuna da bidiyo na kasuwanci na da na tallata da yawa. Na rasa ‘memories’ da yawa.
Na haɗu da Engr. Dr. Rabi’u Kwankwaso a gidansa. Shine haɗuwarmu ta kwanaki lokacin da Engr. Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen Gwamnan jihar Kano a karo na biyu 2023. Na samu zuwa ‘Miller Road’ har na samu damar shiga falon Engr. Rabi’u Kwankwaso. Na kuma samu damar yin hotuna da su sanda muka fito waje. A ranar ne Allah ya fara haɗa ni da gawurtaccen lauya ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima Fagge. Shi ma har na samu sukunin yin hoto da shi.
Bayan nan na cigaba da rubuce-rubucena akan abinda ya shafi Kwankwasiyya ko yabo ko kwarzanta ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A dai 2023 na samu damar halartar taro a ‘Miller Road’ na bikin sallah, sannan na samu damar zuwa taron tunawa da namun daji na duniya da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano.
Kazalika a dai 2023 na fito takarar Shugaban ƙaramar Hukumar Kumbotso, wanda ni ban kai ga matakin yin ‘primary election’ ba ko na ce tantancewar zama ɗan takarar ba sakamakon sanda na je Luggard Gidan Kwankwasiyya siyen for masu siyar da fom ɗin shugabancin ƙaramar hukuma ɗin sun faɗa min ai a yau aka gama tantance ’yan takarar shugaba na Kumbotso ka zo a makare, sai dai ko idan za ka iya gwadawa ka sayi fom dɗin yau tunda Alhamis ne, Juma’a gobe ko Asabar ka gwada kai fom ɗin sakatariyar Kumbotso ko za su karɓa su tantance ka kai ma.
To, duk fa da wannan gwagwarmayar har yanzu akwai masu ganin ai ni ba ɗan Kwankwasiyya ba ne; ɗan shan kai ne, bayan ni kuma ba wani abu na ke nema ba illa kawai son ciyar da jiharmu gaba. Ina jin akwai wasu na tunanin zama ɗan Kwankwasiyya shine ka yi ta yawan wallafa hotunanka da jar hula ko wasu kalamai na bambaɗancin siyasa, wanda kuma ni gaskiya a zahiri hoto bai cika damina ba, duk wanda ya san ni ya san sai ya zama dole ma nake so a san ni a zahiri, kullum ƙoƙarin ɓoye kaina da fuskata nake ba, don wani abu ba sai don kawai haka ra’ayina da ‘style’ ɗina yake.
Sannan Ina da yawan surutu a takarda ko a ‘computer’, amma a zahiri zan iya kwana da yini da mutum muna waje ɗaya ba lallai mu yi hira sosai da shi ba. Amma kuma idan ’yan maganar suka motsa na kan iya kwana Ina hira.
Sannan a cikin wannan tafiyar ta Kwankwasiyya akwai mutanen da na sani a zahiri sani ya kafin haɗuwar siyasa.
Akwai irinsu; Sani Igwe (S. A Farm Center), Jamilu Gama ( MD Farm Center), Akibu Isah Murtala (S.A ), Isma’il Danmaraya ( Kwamishina Finance), Abdulkarim Abdussalam (Tsohon Accountant now Kwamishina), Baba Halilu Dantiye ( Tsohon Kwamishina) da sauransu.
To, duk cikinsu wallahi babu wanda bayan an ba shi muƙami na je wajensa.
Kwankwasiyya ta a raina take da zuciyata da kuma jinin jikina ba don a ba ni kuɗi ko wani abu nake yi ba. Kawai ra’ayina ne hakan.
Baya ga haka ma a 2023 kusan duk rabi da rabin Kano wallahi ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, kowa ɗan Kwankwasiyya ne, saboda an gaji da mulkin Gandujiyya a wancan lokacin.
Don haka babu wani da wanda yake tunanin ni ba ɗan Kwankwasiyya ba ne da mai tunani shine; to yau dai ga shi nan na faɗa.
Kuma insha Allahu idan Allah ya gwada mana lokaci 2027 ya ba mu rai da lafiya zan sake fitowa takara a Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya, don sake gwada sa’ata.
Khairan insha Allah.
Abdullahi Jibril Dankantoma (Uncle Larabi) marubuci ne kuma manazarci
Juma’a, 10 ga Janairu, 2025