Wasu sojoji sun kashe ɗan sanda a Legas

Wasu da ake zargin sojoji ne, sun kashe wani ɗan sanda a anguwar okokomaiko da ke ƙaramar hukumar Ojo, jihar Legas.

Ɗan sandan da abin ya auku gareshi, yana tare da ƴan uwanshi su huɗu a lokacin da suke yawon rangadi.

Hayaniyar ta fara lokacin da yan sandan suka tare wani ɗan achaba kan titin Igbo-Elerin dalilin ya karya dokokin hanya.

Daga bisani da ɗan achaɓan da fasinjan da ya ɗauko suka ƙi tsayawa domin sunce su sojoji ne. A dalilin haka hayaniya ta tashi, wanda ta tabbata cewar sojan ne.

Daga baya, yan uwan sojan suka zo wanda suka taimaka masu wajen hayaniyar. Ans tsaka da haka, sai ɗan sandan ya yanke jiki ya faɗi a cewar mai magana da yawun ‘ƴan sandan jihar Legas Benjamin Hundeyin.