Wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gabanin ƙaddamar da Majalisar Dokokin Ƙasar karo na 10 a watan Yuni, wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman shugabancin majalisar.

Ana sa ran masu neman kujerun majalisar dattawa da ta wakilai za su fara bayyana sha’awarsu a kan muƙaman da suka zaɓa da zarar majalisar dokokin ƙasar ta dawo daga hutun zace a ranar 20 ga watan Maris.

Baya ga shugabancin majalisar dattawa, sauran muqaman da za a naɗa sun haɗa da kakakin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa da kuma manyan muƙamai.

Bisa al’adar majalisa, manyan mambobi – ‘yan majalisa masu wa’adi biyu ko fiye suna jagorancin majalisar.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da kwamishinonin zaɓe a Abuja ranar Asabar cewa, zaɓaɓɓun sanatoci za su karvi takardar shaidar cin zaɓe ranar Talata, yayin da takwarorinsu na majalisar wakilai za su samu nasu ranar Laraba.

Ya zuwa yanzu, a cewar shugaban INEC, jam’iyyar APC ta lashe kujeru 57 na sanatoci, jam’iyyar PDP ta samu 29, jam’iyyar Labour ta samu shida, yayin da NNPP da SDP suka samu biyu kowanne.

A ɗaya ɓangaren kuma, jam’iyyar APGA da YPP ta samu kujera ɗaya.

A majalisar wakilai, APC ta samu kujeru 162 daga cikin kujeru 360, PDP ta samu 102, LP, 34, NNPP 18, APGA huɗu, SDP da ADC sun samu biyu kowanne, yayin da YPP ta samu kujera ɗaya.

Fitattun mutanen da suka nuna sha’awar zama shugaban majalisar dattawa ta 10 sun haɗa da zaɓaɓɓen sanata Ali Ndume, Akpabio (Akwa Ibom), Orji Uzoh Kalu (Abiya), Jibrin Barau (Kano) da Mohammed Sani Musa (Neja), da sauransu.

Ndume wanda ya tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa ta 9 da Danjuma Goje da Lawan, ya tabbatar a ranar Lahadin da ta gabata cewa shi ma yana cikin takarar shugabancin majalisar.

Ya ce, “Akpabio (Akwa Ibom), Orji Uzoh Kalu (Abia), Jibrin Barau (Kano) da Mohammed Sani Musa (wanda ya zo na farko daga Neja) sun tuntuve ni a kan muqamin.

“An tabbatar min cewa Abdulaziz Yari (wanda ya fara zama daga Zamfara) shi ma yana sha’awar, amma bai tuntuɓe ni ba. Amma ku sani ni ma ina cikin tseren; don haka ku sanya fifiko a kaina a cikin rahotonku,” inji sanatan cikin zolaya.

Ya ce, za a iya samun ƙari, amma ya bayyana cewa waɗanda ya ambata su ne suka nuna sha’awarsu ga wannan matsayi.

Da aka tuntuvi Barau ya ce, yana cikin tseren. “Eh, ina cikin tseren. Ina tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa. A yi min fatan alheri.”

A martanin da ya mayar, mai taimaka wa Kalu kan harkokin yaza labarai, Emeka Nwala ya ce, shugaban nasa na sha’awar shugabancin majalisar dattawa amma yana auna wasu abubuwa.