Wata ƙabila da ke fifita rayuwar dabba akan ta mutum

Sanin kowa ne cewa abin al’ajabi ba ya ƙarewa a duniya, domin kuwa ga wata ƙabila da ke fifita rayuwar dabba a kan ta mutum, waɗanda su ke ganin da dabba ta shiga cikin wahala gara ace mutum ne ɗan adam ya shiga. Ita dai wannan ƙabila ba wata ba ce fyace al’ummar ‘Rabari’ da ke garin Gujarant ta cikin yankin ƙasar Indiya.

Al’ummar ‘Ribari’ sun kasance makiyaya ne, ma’ana masu kiwon dabbobi daga wani ɓangare zuwa wani vangare na yankin ƙasar domin nema wa dabbobinsu abinci, basu da takamaiman wajen zama guda ɗaya kasancewar su dai ba mazauna waje ɗaya ba ne, su na kiwon dabbobi kamar shanu, tumakai, awaki, raƙuma da dai sauran dabbobin gida da aka san su.

Abu mafi ban mamaki ga wannan al’umma shi ne da a ce yau an wayi gari wata dabba daga cikin dabbobinsu ya kwana da yunwa, gara ace ɗaya daga cikinsu bil adama ya kwashe sati guda ba tare da ya sanya koda kwayar hatsi a bakinsa ba.

Turƙashi! Tabbas wannan ɗabi’a ta su abar dubawa ce, su kan bawa dabbobinsu kulawa fiye da da bil adama. Babban tashin hankali ne a gare su ace dabba tana jin yunwa.

Al’adarsu:
A wasu lokutan akan iya hangar mutanen ‘Rabari’ tafe da shanunsu su na kora su a kan tituna tare da iyalansu waɗanda su ke sanye da tufafi irin na su na gargajiya.

Mata daga cikinsu su na hura wutar itace ya ruru sosai domin su yi amfani da shi wajen girki, su na ɗebo ruwa domin yin amfani sannan daga bisani kuma su kan tattare dukkan kayayyakinsu su ɗora a kan raƙuma, akasarinsu za ka gansu sanye da suturunsu ma su kyau, wanda yawanci ya kan kasance kamar gauto, mayafai masu ƙyalli, kayan ado na kawa waɗanda su ka kasance masu ƙara da ɗaukar hankali.

Mazaje daga cikinsu sun kasance masu ɗan duhu, dogaye ne bugu da ƙari kyawawa ne matuƙa.

Mafi burgewa da sha’awa daga waɗannan mutane shi ne, su dai suna yin tufafi, tukwane, kayan kwalliya, da dai sauran kayayyakin amfaninsu na gida da kansu ba tare da sun ce lallai sai wani ya yi sannan su samu ko su saya ba, ma’ana mutane ne masu kirkira kuma su ƙera ababen amfani da kuma buƙatunsu na yau da kullum.

Matansu su na a sahun mata masu ado na bajinta, su kan sanya maka-makan zobba a hancinsu, jibga-jibgan ababen wuya, sannan kuma ga ɗirka-ɗirkan kayan ado na kawata hannaye kamar su, zobe, awarwaro da sarƙar hannu.

Matansu su na sanya tufafi waɗanda kalolinsu ke da hasken gaske, akasari su kan yi amfani da kaya masu haske wanda ya sanya har ake iya bambance matan Rabari daga cikin sauran mata.

Matan aure daga cikinsu su na amfani ne da kayan ado farare misali: farin awarwaro wanda ake sanya shi tun daga tsintsiyar hannu har zuwa kafaɗa, ‘yan mata kuwa su ma ba a barsu a baya ba domin kuwa su ma su kan yi nasu kwalliyar iya bakin gwargwado, su na amfani da zoben ƙafa, sarƙar ƙafa, ‘yankunne, zoben hanci da kuma saqar hannu.


Akwai abin ɗaukar hankali dangane da waɗannan mutane, wannan abu ya kasance wani nau’in zane da a kan yi musu a jiki wanda kuma baya fita (tattoo) akan yi musu zanen abubuwa kamar dangin: maciji, kunama da sauransu. Wannan zane ana yi musu shi a wurare kamar fuska, hannaye, kafafu.

Abinci:
Cimar al’umar dai ta kasance kakkaurar madara ce mai zaƙin gaske, ita wannan madara akan sarrafata ne ta hanyar dafawa a kan wuta mai ƙarancin zafi, sannan kuma sai a bar ta akan wuta ta yi ta dahuwa, zata ɗauki lokaci mai tsawo ta na dahuwa sannu cikin hankali zata yi kauri kuma sai kalarta ta koma ruwan hoda.

Addini:
Al’ummar Rabari sun kasance masu bautar abin bautar hindu ne, wanda suke yi wa laqabi da ‘Krisha’.