Wata baƙuwar cuta ta fara kashe mutane a Sakkwato

Daga UMAR GWARANYO

Gwamnatin Jihar Sokoto ta fidda wata sanarwa mai bayyana ɓarkewar wata sabuwar cuta a wani ɓangare na jihar. Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Gwamna Jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ta bayyana cewa mutane huɗu sun mutu daga cutar.

Haka kuma sanarwar ta nuna adadin mutanen da suke asibiti a halin yanzu suna karɓar magani sun haura 20.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce, “A yanzu haka mutane 24 na karɓar kulawa a asibitoci daban-daban a faɗin jihar. Amma an ƙirƙiri wani kwamiti da nufin bincikar cutar tare da gano maganin ta da rigakafin ta.”

Gwamnan ya ce a madadin gwamnati da ɗaukacin jama’ar jihar, ya nuna alhini da ta’aziyya ga iyalai da dangin ’yan’uwa waɗanda suka mutu.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “A halin yanzu gwamnatin jiha ta tashi da kwamitin ƙwararru, ƙarƙashin jagorancin kwamishinonin lafiya da na muhalli na jihar, da nufin bincikar cutar da gano maganin tare da rigakafin ta.

“Bugu da qari, gwamnati ta ɗauki nauyin kula da mutanen da suka harbu da cutar kuma tana yi musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa tare da komawa ga dangin su da ’yan’uwan su.

Daga nan Gwamna ya umarci jama’a da su kiyaye ɗabi’u na tsafta da kulawa sannan kuma su dage da addu’o’in neman taimakon Allah a wannan lokaci na ƙalubale.