Wata mata ta ci na-jaki a wajen zaɓe a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Masu kaɗa ƙuri’a sun lakaɗa wa wata mata duka a wajen zaɓe bisa zarginta da aka yi da sayen ƙuri’a.

Lamarin ya faru ne a Ado Yola Primary School fa ke mazaɓar Na’ibawa cikin Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano.

Da aka nemi jin ta bakinta, matar ta ce kuɗin mota ta bayar ba kuɗin sayen ƙuri’a ba kamar yadda aka yi zargi.