Watan Ramadana mai albarka

Musulmi a Nijeriya da sauran sassan duniya sun fara azumin watan Ramadana na bana a ranar Asabar 2 ga Afrilu, 2022. Hakan ya biyo bayan sanarwar da Shugaban Majalisar Qoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar da Sarkin ya fitar, wanda aka samu a shafin Tuwita na NSCIA, an samu rahotanni masu inganci cewa, an ga jinjirin watan Ramadan a jihohin Sokoto, Yobe, Zamfara, Katsina, Plateau, Kaduna da Kano da dai sauransu. Ya ce, “bayan tantancewa daga kwamitin ganin wata na ƙasa da kuma tabbatarwa da kwamitocin jihohi, da kuma nazarce-nazarcen yau da kullum suka yi, ina sanar da ganin jinjirin watan Ramadan wanda ke nuna qarshen Sha’aban 1443AH”, ya ƙara da cewa, “kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, al’ummar musulmi za su fara azumi ranar Asabar kamar yadda ya kamata.”

A yayin da ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalar rashin tsaro a ƙasar nan domin samar da zaman lafiya ga ’yan ƙasa da ci gaban al’umma, Sarkin ya kuma shawarci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan damar na azumin bana wajen addu’ar Allah ya cigaba da ba mu zaman lafiya da cigaban ƙasa. Ya kuma umurci musulmi muminai da su sadaukar da kansu ga ibadar Allah a tsawon wannan wata mai alfarma. Ya kuma yi kira da a dage da yi wa shugabanni addu’o’i don ba su damar jagorantar ƙasar nan zuwa ga cigaba.

“Muna ƙara kira ga ‘yan Nijeriya da su cigaba da zama lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini da ƙabilanci ba,” inji shi.

Sarkin ya kuma shawarci masu hannu da shuni da su taimaka wa talakawa tare da jaddada buqatar a ƙara haƙuri da ’yan uwantaka a Nijeriya.

Yin azumin watan Ramadan a wata na tara na kalandar Musulunci na ɗaya daga cikin ƙa’idoji biyar na Musulunci waɗanda idan ba yi su ba imanin mutum ga addinin Musulunci zai kasance bai cika ba. A Musulunci, azumin Ramadan ya ƙunshi kamewa daga ci, sha, shan taba, tsakanin alfijir da faɗuwar rana na tsawon watan Ramadan. Umurnin wannan farilla na addini yana cikin Alƙur’ani sura 2:183 inda Allah Maɗaukakin Sarki ya ke cewa, “Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke a gabaninku, tsammaninku. Ana azumin watan Ramadan na kwanaki 29 ko 30, gwargwadon lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal, wata na goma a kalandar Musulunci.

Baya ga nisantar abinci a jiki baya ga wasu hane-hane da aka yi wa muminai a lokacin azumin watan Ramadan, an kuma umurci musulmi da su yi amfani da wannan lokaci mai alfarma wajen nuna kyawawan halaye na haƙuri da karimci da sadaka da kyautatawa musamman ga marasa galihu a cikin al’umma. Don haka ake kwaɗaitar da su da yin sadaka, ciyar da miskinai da kuma kiran sauran waɗanda ba musulmi ba domin buɗa baki da su. Aikin alherin da ake yi a watan Ramadan yana samar da ingantacciyar fahimta ta addini, daidaito da kuma haɗin kan al’umma, waɗanda dukkansu sun fi so ga al’umma masu yawan imani da mabanbantan ra’ayi irin Nijeriya.

Azumin Ramadan yana baiwa mumini na kwarai hakuri da juriya. Idan musulmi ya yi azumi, yana iya jin raɗaɗin yunwa ko ƙishin ruwa amma a haƙura. Wannan raɗaɗi da juriya, ko da ya ke na ɗan lokaci ne, suna sa mutum ya san irin halin da wasu da yawa ke fama da su, waɗanda wataƙila suna rayuwa a cikin ƙunci tare da aarancin samun abubuwan buƙatun rayuwa.

Jigon wannan wata yana buƙatar musulmi da su yi tawali’u a cikin duk abin da suka shagaltu da su. An ƙarfafa su da kada su ci abinci kuma su kiyaye faɗi kuma su kwana cikin ibada. Ya kamata al’ummar Musulmi a Nijeriya a matsayinsu na shugabanni, su yi amfani da damar da watan Ramadan ke da shi wajen nisantar duk wata munanan ɗabi’u da ta addabi ƙasar nan da kawo cikas ga burinta na zama mai dogaro da kai da cigaban gaske.

Muna kira ga malamai da masu wa’azi da su kasance masu gaskiya ga kiran da suke yi a matsayinsu na shugabanni a cikin al’umma, da sauran masu kula da yanayi na musamman a ƙasar. A nisanci kalamai ko maganganu masu zafi da tunzura a cikin tafsirinsu na Alƙur’ani da sauran littattafan addini.

Kyakyawar wa’azi a Musulunci yana buƙatar a yi amfani da hikima da kalmomi masu kyau. An shawarci masu wa’azi da su ilimantar da masu sauraronsu a kan kyawawan halaye na amfani da hanyoyin da ba na tashin hankali ba don samar da zaman lafiya mai ɗorawa a ƙasar.

Ramadan yana kira ga barin kwaɗayi. Muna kira ga dillalan kayan masarufi da kada su yi amfani da lokacin Ramadana da bai kamata ba wajen cin riba ta hanyar qara farashin kayan abinci wanda tuni ya kankama.
Blueprint Manhaja na yi wa ɗaukacin al’ummar Musulmi barka da azumin watan Ramadana.